Saraki ya bada labarin zamansa Shugaban Majalisa a 2015 duk da adawar Bola Tinubu a APC

Saraki ya bada labarin zamansa Shugaban Majalisa a 2015 duk da adawar Bola Tinubu a APC

  • Abubakar Bukoka Saraki ya ziyarci Legas domin ya yi zama da ‘ya ‘yan PDP a kan batun takara
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya fadawa ‘yan jam’iyyarsa yadda ya kara da Bola Tinubu
  • A 2023, Saraki yana ganin bai da wanda ya fi shi dacewa da rikon Najeriya a kaf PDP da kuma APC

Lagos - A ranar Litinin, 9 ga watan Mayu 2022, Abubakar Bukoka Saraki ya yi zama da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na reshen jihar Legas kan batun takararsa.

Daily Trust ta ce Dr. Abubakar Bukoka Saraki ya yi kira ga jagororin jam’iyyar hamayyar da su mara masa baya ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a 2023.

Tsohon shugaban majalisar dattawan kasar ya yi wa ‘yan PDP bayanin yadda ya karya daular Bourdillon.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Legit.ng Hausa ta fahimci Bukoka Saraki yana magana ne game da babban jigon APC na kasa, kuma tsohon gwamna na jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu.

Ko da bai kama suna ba, Saraki ya nuna cewa Asiwaju Bola Tinubu ya yi yunkurin hana shi zama shugaban majalisar dattawa bayan sun kafa gwamnati a 2015.

A lokacin Saraki yana jam’iyyar APC mai mulki da rinjaye, ya nemi zama shugaban majalisa, amma jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu ya nuna adawarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saraki
Bukola Saraki yana Shugaban Majalisa Hoto: medium.com/@SPNigeria
Asali: UGC

Bourdillon ta je kasa - Saraki

“Dukkaninku kun san cewa ni ne mutum na karshe da ya karya Sarkin Bourdillon, wanda ya ce ba zan zama shugaban majalisar dattawa ba.”
“Ni kuma na ce ‘A’a, sai na zama shugaban majalisar dattawan Najeriya.’ – Bukola Saraki.

PDP za ta karbe Legas a 2023

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Jaridar Pulse ta rahoto Saraki yana cewa jam’iyyar hamayyar za ta karbe mulki daga hannun APC a 2023 Legas. A tarihi dai PDP ba ta taba rike jihar Legas ba.

“Sannan ku san cewa zan jajirce wajen gwabzawa, kuma da yardar Ubangiji a zaben 2023, jam’iyyar PDP za ta karbe mulki a jihar Legas.”
“Za mu karbe jihar Legas. Mun fara wannan da yunkurin sasanta rigingimun da ake yi.”

- Bukola Saraki

Tsohon gwamnan na Kwara ya shaidawa masu zaben ‘dan takaran cewa duk APC da PDP, babu wani mai neman mulki da ya fi shi cancanta ya rike Najeriya.

Ganduje yana son zama Sanata

Ku na da labari Gwamnoni kusan 7 suke shirin tafiya Majalisar Dattawa a 2023. A makon nan aka ji Gwamna Abdullahi Ganduje yashiga takarar Sanata a APC.

Hakan yana nufin kujerar Sanata Barau Jibrin wanda aka fi sani da Maliya ta na yawo a iska domin zai kara ne da Dr. Abdullahi Ganduje a Arewacin Kano.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya na sa ran doke Tinubu, Amaechi da kowa a APC, ya zama ‘dan takara a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng