'Wani Gwamna mai ci ne ya tura kuɗin' Gaskiyar yadda aka Saya wa Jonathan Fom N100m ta fito

'Wani Gwamna mai ci ne ya tura kuɗin' Gaskiyar yadda aka Saya wa Jonathan Fom N100m ta fito

  • Gaskiyar bayani kan yadda aka karɓan wa tsohon shugaba, Goodluck Jonathan, Fom ɗin APC kan N100m ta fito fili
  • Rahoto ya nuna cewa wani gwamna mai ci ne ya tura kuɗin zuwa Asusun da APC ta tanada don tara kuɗin a Bankin Heritage
  • Da farko dai an bayyana cewa gamayyar kungiyoyin arewa ne suka lale kuɗin suka siya wa Jonthan Fom ɗin takarar shugaban ƙasa

Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta karɓi miliyan N100 cas a asusunta na siyawa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, Fom ɗin takara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Jaridar ta bayyana cewa wani gwamna dake kan kujerarsa a Najeriya ne ya tura Miliyan N100m zuwa Asusun jam'iyyar APC da ke Bankin Heritage.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Yadda aka saya wa Jonathan Fom.
'Wani Gwamna mai ci ne ya tura kuɗin' Gaskiyar yadda aka Saya wa Jonthan Fom N100m ta fito Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Lambar asusun da aka tura wa waɗan nan kuɗi na Fom ɗin sha'awa da tsayawa takara a Bankin shi ne, 5600007616.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa takardar shaidar biyan Kuɗin Bankin na ɗauke da Adireshin Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC ta ƙasa.

Takardar ta ce:

"Mun rubuto domin tabbatar da cewa an saka Miliyan N30m a wannan asusun na Fom ɗin nuna sha'awar takarar Goodluck Jonathan."

A takarda ta biyu duk daga Bankin ta shaida wa jam'iyyar APC cewa miliyan N70m sun sake shiga asusun na Fom ɗin tsayawa takarar Mista Jonathan.

Jonathan wanda har yanzun bai bayyana sauya sheka zuwa APC ba a hukumance, har zuwa yanzu bai yi martani kan Fom ɗin ba.

Takardar biyan kudin

A kwanakin baya, wasu dandazon yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a Ofishin sa, inda ya kwantar musu ɗa hankali da cewa, 'ku zuba ido.'

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Tun da farko dai, mun kawo muku rahoton cewa gamayyar kungiyoyin arewa ne suka haɗa kudi suka karban wa Jonathan Fom na takara a APC.

A wani labarin kuma Babban Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga mukaminsa, ya sayi Fam ɗin fafatawa a 2023

Hadimin gwamnan jihar Ekiti kan harkokin kwadugo, Oluyemi Esan, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Mista Esan ya ɗauki wannan matakin ne domin ya samu damar neman takarar ɗan majalisar wakilai a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262