Babban Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga mukaminsa, ya sayi Fam ɗin fafatawa a 2023

Babban Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga mukaminsa, ya sayi Fam ɗin fafatawa a 2023

  • Hadimin gwamnan jihar Ekiti kan harkokin kwadugo, Oluyemi Esan, ya yi murabus daga kan kujerarsa
  • Mista Esan ya ɗauki wannan matakin ne domin ya samu damar neman takarar ɗan majalisar wakilai a zaɓen 2023
  • Ya gode wa gwamnan bisa damar da ya ba shi na ba da gudummuwa a gwamnatinsa, ya sayi Fom na APC

Ekiti - Babban mashawarcin gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti kan harkokin kwadugo, Oluyemi Esan, ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Premium Times ta rahoto cewa hadimin gwamnan ya yi haka ne domin samun damar neman takarar mamba mai wakiltar Ado/Irepodun/Ifelodun Central 1 a majalisar dokokin tarayya.

Wannan na kunshe ne a wata wasika da ya sa wa hannu kuma ya aike wa gwamna a Ado Ekiti, babban birnin jihar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.
Babban Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga mukaminsa, ya sayi Fam ɗin fafatawa a 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Esan ya gode wa gwamna Fayemi bisa alfarmar da ya masa na ba shi dama ya ba da gudummuwa a gwamnatinsa.

Vanguard ta rahoto Ya ce:

"Bisa haka, na yi murabus daga muƙamina na babban mashawarci kan harkokin kwadugo ga mai girma gwamna, kuma na ƙagu na samu wata damar aiki tare da shi yayin da nake wakilatar mutane na."

Tsohon hadimin ya Sayi Fom

Tsohon hadimin gwamnan ya sayi Fom ɗin tsayawa takarar kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Ado/Irepodun/Ifelodun Central 1.

Mista Esan ya ce ya yanke shawarar neman takarar ne saboda tsanani. kaunar da yake da ita na ya sadaukar da kansa wajen yi wa al'umma aiki da samar musu da wakilci mai kyau karkashin APC.

Kara karanta wannan

Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu jiga-jigan FG su yi murabus

Tsohon shugaban kwadugon ya ce wakilci mai kyau ke kawo kyakkyawan jagoranci, inda ya tabbatar da ba da kan sa wajen yi wa al'ummar mazaɓarsa aiki.

Bugu da kari, ya ce ya shiga tseren takarar ɗan majalisa ne domin amsa kiran da mutanen mazaɓarsa suka jima suna masa.

A wani labarin kuma Barau ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai fafata da Ganduje a 2023

Rikicin siyasa a jihar Kano kuma a jam'iyyar APC ya ƙara ɗaukar wani sabon babi tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje.

Sanata mai wakiltar Kano ta arewa kuma ɗan tsagin Shekarau ya sayi Fom ɗin takarar Sanata, wacce Ganduje zai nema a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel