Rikicin APC a Kano: Ɗan Majalisa, Abdulkadir Jobe Ya Fice Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili

Rikicin APC a Kano: Ɗan Majalisa, Abdulkadir Jobe Ya Fice Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili

  • Abdulkadir Jobe, Dan majalisar Kano mai wakiltan mazabun Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa ya fice daga APC
  • Jobe, ya ce ya fice daga jam'iyyar mai mulki ne saboda rigingimun cikin gida da ke faruwa a APC ta Kano
  • Duk da cewa Jobe bai sanar da jam'iyyar da zai shiga ba, an ga hotonsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin wata ziyara da kai masa a ranar Juma'a

Dan majalisar wakilai na tarayya daga Jihar Kano, Abdulkadir Jobe, ya yi murabus daga jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa, Premium Times ta rahoto.

Mr Jobe, wanda ke wakiltar mazabun Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa ya ce ya fice daga jam'iyyar ne saboda rikicin cikin gida da ake yi a jam'iyyar reshen Kano.

Rikicin APC a Kano: Dan Majalisa, Abdulkadir Jobe Ya Fice Daga Jam'iyyar APC
Dan Majalisa, Abdulkadir Jobe Ya Fice Daga Jam'iyyar APC. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Jobe bai ambaci sabuwar jam'iyyar da zai koma ba

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Amma, bai bayyana cewa ko zai shiga wata jam'iyyar siyasar ba. Sai dai, an ga hotonsa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP bayan wata ziyara da ya kai masa a ranar Juma'a a gidansa da ke Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rikicin cikin gida na APC a Kano yasa na yi murabus - Jobe

Mr Jobe, cikin wasikar murabus da ya aika wa shugaban jam'iyyar APC a mazabarsa ta Joben Kudu ya ce:

"Ina rubuta wannan ne domin sanar da murabus di na daga jam'iyyar APC a hukumance daga ranar Alhamis 5 ga watan Mayun 2022.
"Bayan tuntuba da magoya baya na da abokan siyasa, mun ga cewa babu amfani mu cigaba da zama a APC saboda rikicin da ke faruwa a jihar Kano a yanzu.
"Duk da haka, na goda bisa damar da aka bani na yi wa al'ummar mu hidima," a cewar Mr Jobe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Premium Times ta rahoto cewa ficewar Jobe ya biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke ne na mika wa sashin Gwamna Abdullahi Ganduje shugabancin jam'iyyar bayan watanni ana shari'a.

Bangarorin biyu sun yi zabe biyu a ranar 18 ga watan Oktoba, inda tsagin tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ta zabi Haruna Danzago a matsayin shugaba yayin da tsagin Ganduje ta zabi Abdullahi Abbas.

Yan tsagin sun hada da Barau Jibrin, sanatan Kano ta Arewa, da yan majalisar wakilan tarayya hudu daga jihar da suka hada da Nasiru Abdua, Abdulkadir Jobe, Sha'aban Sharada da Haruna Dederi.

Kwankwaso: NNPP Za Ta Samu Gaggarumin Nasara a Zaɓukan 2023

A bangare guda, tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, za ta samu gaggarumin nasara a zabukan shekarar 2023.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Kwankwaso ya bada tabbacin ne ga magoya bayan jam'iyyar a yayin taron majalisar shugabannin jam'iyyar da aka yi a ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

Kwankwaso, wanda ya ce yan Nigeria suna kara shiga jam'iyyar, ya shawarci saura su yi rajista kuma su nemi kujerar takara da suke so a zaben 2023 a karkashin jamiyyar.

Dan majalisar wakilai na tarayya daga Jihar Kano, Abdulkadir Jobe, ya yi murabus daga jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164