Kwankwaso: NNPP Za Ta Samu Gaggarumin Nasara a Zaɓukan 2023
- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, jogaran jam'iyyar NNPP (mai kayan marmari) na kasa ya ce jam'iyyar za ta samu gaggarumin nasara a zabukan 2023
- Kwankwaso ya furta haka ne yayin taron jam'iyyar a Abuja yana mai shawartar magoya bayan jam'iyyar su tafi mazabansu su yi rajitsa sannan masu sha'awar takara su siya fom don babu tsada
- Rufai Alkali, Shugaban jam'iyyar ta NNPP na kasa ya ce abin da jam'iyyar ta sa a gaba shine ceto demokradiyya da Najeriya daga halin da suka shiga
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, za ta samu gaggarumin nasara a zabukan shekarar 2023.
Daily Nigerian ta rahoto cewa Kwankwaso ya bada tabbacin ne ga magoya bayan jam'iyyar a yayin taron majalisar shugabannin jam'iyyar da aka yi a ranar Asabar a Abuja.
Kwankwaso, wanda ya ce yan Nigeria suna kara shiga jam'iyyar, ya shawarci saura su yi rajista kuma su nemi kujerar takara da suke so a zaben 2023 a karkashin jamiyyar.
"Bari in tunatar da yan Najeriya cewa ana sayar da fom na takarar majalisar jiha da wasu mukaman a sakatariyar jam'iyyar na kasa ga wadanda ke son yin takara.
"Ina karfafa wa kowa gwiwa ya zama irin mu a nan; zama mutane masu hangen nesaa kasar nan. Wannan jam'iyyar na masuu kishin kasa ne.
"Muna son kowa ya tafi mazabarsa ya yi rajista. Fom din babu tsada. Tabbas ba N100m bane don fom din takarar shugaban kasa da sauransu," in ji shi.
Kazalika, a jawabinsa, shugaban NNPP na kasa, Rufai Alkali, ya ce abin da jam'iyyar ta sa a gaba shine ceto demokradiyya da Najeriya.
Alkali ya ce kallubalen da ke gaban Najeriya mai girma ne amma abu ne mai yiwuwa.
'Dan Majalisar Kano Ya Yi Watsi Da Kwankwasiyya, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC
A bangare guda, 'Dan Majalisar Jihar Kano mai wakiltan Kano Municipal, Salisu Gwangwazo, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP ya kuma koma APC.
Daily Nigerian ta rahoto cewa Gwangwazo da aka fi sani da Alhajin Baba, ya sanar da sauya shekarsa ne cikin wata wasika da ya aike wa Kakakin Majalisar Kano, Hamisu Chadari, a ranar Juma'a.
Sanarwar da babban sakataren watsa labarai, na Majalisar Jihar Kano, Uba Abdullahi ya ce dan majalisar ya fice daga PDP ne saboda rikicin da ake fama da ita.
Asali: Legit.ng