Yanzu-yanzu: Abdulmumini Jibrin ya fadi ba nauyi, Ali Datti ya lashe zaben

Yanzu-yanzu: Abdulmumini Jibrin ya fadi ba nauyi, Ali Datti ya lashe zaben

- Hanarabul AbdulMumini Jibrin ba zai koma majalisar wakilan tarayya ba

- Tsohon dan majalisa ya fadi ba nauyi a zaben mai-mai da aka gudanar a ranar Asabar

- Masu sharhi sun bayyana cewa Jibrin ya fadi ne sakamakon fito-na-fito da yayi da shugabannin APC a jihar

Tsohon dan majalisan wakilan tarayya, AbdulMumini Jibrin, ya fadi ba nauyi a zaben mai-mai da aka gudanar a mazabar Kiru/Bebeji na jihar Kano.

Jibrin wanda yake dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya sha kasa hannun abokin hamayyarsa Alhaji Ali Datti Yako, na Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar 25 ga Junairu, 2020.

Baturen zaben, Farfesa Abdullahi Arabi, ya ce Ali Datti ya samu kuri'u 48,641 yayinda AbdulMumini Jibrin ya samu kuri'u 13,507.

Yanzu-yanzu: Abdulmumini Jibrin ya fadi ba nauyi, Ali Datti ya lashe zaben
Sakamakon
Asali: Facebook

Kafin faduwarsa wannan karon, Abdul Mumini Jibrin ya kasance a majalisar wakilai tun shekarar 2011 a matsayin dan PDP amma daga baya ya sheka APC.

Gabanin zaben nan, dan siyasan ya shiga takun saka da shugabannin jam'iyyarsa a jihar Kano.

Wani shahrarren dan APC a Tuwita, D Olusegun, ya bayyana cewa: "Tun lokacin da dogaran Ganduje suka hana AbdulMumini Jibrin, zuwa taya gwamnan murnar nasarar zabe a kotun koli, na san da wuya ya sake komawa (majalisa)."

Wani AbdulAziz Bakare yace: "Bisa ga rahotanni, shugabannin APC sun yanke shawarar goyon bayan dan takarar PDP a zaben sabanin dan jam'iyyarsu Abdulmumini Jibrin da alkawarin cewa dan PDPn zai koma APC bayan nasara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel