Da Dumi-Dumi: Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya Ya Shige Jerin Masu Son Kujerar Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya Ya Shige Jerin Masu Son Kujerar Buhari a 2023

  • Dimeji Bankole, Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya ya biya N100m lakadan ya karbi fom din takarar shugaban kasa a APC a zaben 2023
  • Mahmud Shinkafi, tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne da wasu jiga-jigan APC suka karbi fom din a madadin Dimeji Bankole
  • Wani na kusa da tsohon kakakin majaliar, Malam Abdullahi Bayero, shima ya tabbatar da siyan fom din a madadin Bankole

Tsohon kakakin majalisar wakilatai na tarayya, Dimeji Bankole, ya shiga jerin wadanda suka siya fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashi jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Premium Times ta tattaro cewa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Mahmud Shinkafi ne ya karbi fom din takarar kan N100m a madadin Mr Bankole.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Da Dumi-Dumi: Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya Ya Shige Jerin Masu Son Kujerar Buhari a 2023
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya Ya Shige Jerin Masu Son Kujerar Buhari a 2023. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Malam Abdullahi Bayero, wani na kusa da tsohon kakakin majalisar tarayyar, shima ya tabbatar da siyan fom din a madadin Bankole, rahoton The Punch.

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi wa Shinkafi rakiya.

Mr Bankole ya tabbatar da lamarin amma ba yi wani karin bayani ba.

Na kammala tuntuba, kuma na samu goyon baya daga masu ruwa da tsaki - Bankole

Idan za a iya tunawa a makon da ta gabata tsohon kakakin majalisar, Bankole ya ce ya kammala tuntubar muhimman masu ruwa da tsaki a sassan kasar.

Bayero ya ce:

"Right Honarabul Dimeji Bankoe ya shiga takarar kuma karkashin jam'iyyar APC mai mulki. Ya gana da masu ruwa da tsaki da dama kuma sun bashi hadin kai sosai, musamman a arewa, don hakan zai siya fom sati mai zuwa.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

"Mutane da dama na yi masa kallon cewa ya cika sharruda da yawa idan ana maganar matashi, mai basira, cancanta da shugaban kasa mai kishin kasa.
"Kamar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce, Najeriya, na bukatar matashin shugaba. Ina ganin bai kamata a tsaya muhawarra ba duk da kundin tsarin mulki bai hana dattawa takara ba.
"Akwai yan arewa da dama da suka yi imanin cewa Bankole shine ya dace, idan aka duba yadda ya tafiyar da abubuwa lokacin da marigayi Yar'adua ke jinya. Shine dan takarar da arewa da sauran yankunan Najeriya za su amince da shi."

Bankole wanda ya yi takarar gwamnan Ogun a jam'iyyar ADC, ya yi rajista a APC a watan Maris na 2021.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel