Mace ta farko da ta tsaya takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC ta lale miliyoyi ta sayi Fom

Mace ta farko da ta tsaya takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC ta lale miliyoyi ta sayi Fom

  • Yar takarar shugaban ƙasa mace da ta bayyana aniyarta a APC, Uju Ohanenye, ta biya kuɗi ta karɓi Fom a Abuja ranar Alhamis
  • A jawabin da ta yi, ta ce ba zata tsaya wani ɗan takara ya ba ta tsoro ba domin yan Najeriya uwa suke buƙata a halin da suke ciki
  • Sai dai tace a shirye take ta janye takara ga wanda ta amince zai iya magance talauci da rashin tsaro

Abuja - Mace ta farko kuma ɗaya tilo da ta ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC, Uju Ohanenye, ta tabbatar da aniyarta ranar Alhamis yayin da ta Sayi Fom ɗin takara a Abuja.

Ta shaida wa manema labarai bayan ta karɓi Fom cewa mazan da ke neman shugabancin ƙasa a APC ba zasu yi nasarar tsoratar da ita ba.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Mis Uju Ohanenye.
Mace ta farko da ta tsaya takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC ta lale miliyoyi ta sayi Fom Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto Ohanenye na cewa:

"Abin da nake tsoro shi ne abokan takarata maza za su yi duk me yuwuwa su fitar da ni, amma na tsaya kan kafafuna saboda al'umma ta kuma na zo ne na kare su. Za su so ture ni gefe amma ba zan tsorata ba."

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa APC na sayar da Fom ɗin sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa kan kuɗi Miliyan N100m.

Yan takara mata, matasa da kuma nakasassu da ke neman wani ofishin siyasa ƙarƙashin APC zasu biya kashi 50% na kuɗin wato rabi kenan.

Shin zata iya janye wa daga takara?

Mis Ohanenye ta ce tana da duk wani abu da ake bukata ta jagoranci ƙasar nan zuwa matakin cigaba kamar yadda yan takara maza ke da shi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Sai ɗai ta ce a shirye take ta janye wa kowane ɗan takara wanda ke tattare da manufa da kudirin shawo kan talauci da rashin tsaron ƙasar nan.

Yar takaran ta kuma jaddada cewa a matsayinta na uwa, ta san hanyoyin da zata bi wajen saita komai ya dawo kan hanya. Punch ta rahoto tace:

"A rayuwar yau, duba da rashin tsaro a ƙasa da sauran matsaloli, yara na bukatar uwa da zata kula da su, zamu gane haka daga halayyan su. Na jima a siyasa kuma saboda abinda na gani ya sa na yanke shigowa a dama dani."

A wani labarin na daban kuma Rikicin APC a Kano na dab da zuwa karshe, Kotun Koli zata yanke hukuncin raba gardama tsakanin Ganduje da Shekarau

Kotun koli zata bayyana hukuncin ƙarshe kan rikicin APC a Kano tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau gobe Jumu'a.

Rikici ya ɓarke a APC reshen Kano har ta kai dare wa gida biyu, tsagin masoyan gwamna da tsagin G-7 na Sanata Shekarau.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Shugaban APC ya magantu kan shirin sauya shekar Jonathan zuwa jam'iyyar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262