Yanzu Yanzu: Ba za a tsawaita wa'adin zaben fidda gwani ba – INEC ga jam’iyyun siyasa
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar da jam'iyyun siyasa cewa ba za ta tsawaita wa'adin zaben fidda gwani ba
- INEC ta ce jam'iyyu na da sauran wata daya daga yanzu domin gudanar da zabukan fidda yan takararsu na mukamai daban-daban
- Kamar yadda aka tsara tun da farko, wa'adin zai cika ne a rana Juma'a, 3 ga watan Yunin shekarar nan
Abuja - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ce wa’adin da aka kayyade don gudanar da zaben fidda gwani na nan daram a kan Juma’a, 3 ga watan Yuni.
Hukumar zaben ta ce jam’iyyun siyasa na da sauran wata daya cif daga yau domin kammala zaben fidda gwaninsu, jaridar The Cable ta rahoto.
A cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, INEC ta ce an baiwa dukkanin jam’iyyun siyasa guda 18 sanarwar da yakamata wanda ke nuna ranakun gudanar da babban taronsu.
Hakazalika takardar sanarwar na dauke da ranakun gudanar da zaben fidda gwaninsu na mukamai daban-daban.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamishinan zabe kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ya ce a gabatar da sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya tsakanin 10 zuwa 17 ga watan Yuni.
Okoye ya kara da cewa na gwamnoni da na majalisun jihohi za su kasance daga ranar 1 zuwa 15 ga watan Yuli, rahoton Daily Trust.
INEC ta karyata Tinubu a karo na 2 a wata 1, ta yi wa jigon APC martani kan batun katin zabe
A wani labarin, shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi karin haske a game da wani jita-jita da ke ta faman yawo a kasar nan.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Farfesa Mahmood Yakubu yana musanya ikirarin cewa katin kada kuri’a watau PVC ya kan tashi daga aiki idan har ya dade.
Da yake jawabi a garin Abuja a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu 2022, shugaban hukumar zaben na kasa ya ce katin ba su da ranar daina aiki a Najeriya.
Asali: Legit.ng