Da Dumi-Dumi: Wani Sanatan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
- Sanata Ibikunle Amosun, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe
- Tsohon gwamna a jihar Ogun ya ce yana da faɗin kwarewa a kowane ɓangare da mataki na gwamnati kuma ya shirya yi wa ƙasa aiki
- Ya ce ya san irin mutumin da Najeriya ke bukata duba da halin da ake ciki kuma ya shirya tsaf ya sa basirarsa wajen magance komai
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.
Sanatan ya sanar da burinsa na zama shugaban ƙasa ne a wani taro da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan tsohon shugaban APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, sun shiga tseren takara.
Punch ta rahoto a jawabinsa Amosun ya ce:
"Faɗin kwarewa ta a ɓangaren zaman kai da gwamnati a jam'iyyun siyasa da ƙawance tsakanin matakan gwamnati biyu, masu doka da masu zartarwa, sune suka haskakamun na fahimci matsalar Najeirya."
"Kuma a shirye nake na sanar da jagoranci wanda zai dunƙule ƙasa, har mu cimma matsayin mu na zama a sahun gaba, ba a nahiyar Afirka kaɗai ba a duniyar baƙaƙen fata."
"A yau, ina mai sanar da manufata ta neman tikitin takarar shugaban kasa a hukumance ƙarƙashin jam'iyyar mu APC. Na san ɗumbin matsalolin da suka yi wa ƙasar mu katutu kuma na san sadaukarwar da ake bukatar shugaba na gaba ya yi."
Meyasa ya shiga jerin yan takara?
Tsohon gwamnan ya ce ya shiga takara ne domin amsa kiran da yan Najeriya daga kowane sashi suka jima suna masa.
"Hakan na nufin na girmama kira mai tarihi da kuma nauyin mu haɗa kai mu tafi tare don cimma nasara, mu ƙara gina imanin mu game da goben ƙasar nan duk da ƙalubalen yan ta'adda da muke fama."
A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC ya yabi ɗan takarar shugaban ƙasan PDP, ya ce yana alfahari da shi
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Ƙatsina ya yabi takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike , kan matakin da ya ɗauka game da IPOB.
Gwamnan ya ce ba zai taɓa mancewa da goyon bayan da mutan Ribas suka ba shi ba lokacin yana kakakin majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng