2023: Kuri’u miliyan 12 na nan yana jiranmu a arewa - PRP
- Jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta bugi kirjin cewa tana da kuri'u miliyan 12 da ke jiranta a yankin arewacin kasar
- PRP ta ce tun farko kuri'unta ne aka ranta ma shugaban kasa Muhammadu Buhari domin mambobinta na neman wanda zai maye masu gurbin Mallam Aminu Kano
- Ta kuma ce ko shakka babu za ta kayar da manyan jam'iyyun kasar guda biyu wato APC da PDP a zabe mai zuwa domin a cewarta tana nan da farin jininta
Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) za ta kalubalanci jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da People’s Democratic Party (PDP) wajen mallakar manyan kujeru a babban zaben 2023, Iliyasu Gadu wani marubuci kuma mai sharhi kan harkokin jama’a, ya yi ikirari.
Gadu, wanda ya yi watsi da ikirarin cewa jam’iyyar bata da karfin fafatawa da manyan jam’iyyun kasar guda biyu, ya ce jam’iyyar na da kuri’u miliyan 12 da ke jiranta a arewa.
Ya yi ikirarin cewa PRP na kuri’u miliyan 12 a arewa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ta tunkaho da su.
Yayin da yake hira a shirin Trust Tv na Daily Politics a ranar Laraba, Gudu ya ce:
“Nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma a yau nasarorin PRP ne a zahirin gaskiya.
“Yana amfana ne daga PRP. Kuri’u miliyan 12 da Buhari ya dogara da su kuri’un magoya bayan PRP ne.”
Ya kara da cewa:
“Magoya bayan PRP na neman Aminu Kano na biyu kuma wannan ne dalilin da yasa suka mikawa Buhari kuri’un. Ba wai sun yi watsi da PRP uwar jam’iyyarsu bane.”
Daily Trust ta kuma rahoto cewa Gadu ya ce PRP na da damar yin nasara a zaben shugaban kasa sosai “saboda mutane sun gane cewa ya zama dole mu koma ga siyasar akida.”
“A tsohuwar jihar Kano da tsohuwar jihar Kaduna, har yanzu nasarorin da suka samu na nan. Kimar jam’iyyar bata canja ba.”
Da yake magana, Babatunde Alli, babban sakataren PRP na kasa ya ce jam’iyyar kadai ce ta rage da kima.
Ya ce, sabanin jam’iyya mai mulki da ke siyar da fom naira miliyan 100, PRP tana siyar da fom din takarar shugaban kasa kan naira miliyan 10.
Yanzu haka: Yan sanda sun kwace sakatariya PDP a wata jahar kudu
A wani labarin, mun ji cewa jami’an yan sanda a safiyar ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, sun karbe sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Abia.
Jami’an tsaron wadanda ke dauke da makamai sun hana ma’aikata da baki shiga harabar sakatariyar wacce ke a unguwar Finbars, Umuahia.
Daya daga cikinsu da aka tuntuba ya ce umurni ne daga sama, jaridar Vanguard ta rahoto.
Asali: Legit.ng