Zaben 2023: Jigon APC ya shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa, zai sayi fom

Zaben 2023: Jigon APC ya shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa, zai sayi fom

  • Gbenga Olawepo-Hashim ya bayyana sha'awarsa ta gaje kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa a karkashin jam'iyyar APC
  • Tsohon dan takarar shugaban kasan a zaben 2019 ya ce zai sayi fom din tsayawa takara ranar Alhamis a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja
  • A cewarsa, ya dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kasar nan kan kudurin nasa

Najeriya - Wani dan jam’iyyar APC mai mulki, Mista Gbenga Olawepo-Hashim ya bayyana aniyarsa ta neman ya gaji kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Olawepo-Hashim wanda ke da sha'awar daga tutar jam'iyyarsa a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa na shirin sayen fom din tsayawa takara a ranar Alhamis 5 ga watan Mayu a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai wacce Legit.ng ta samo.

Jigon APC na son gaje kujerar Buhari
Shirin 2023: Wani jigon APC ya shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa, zai sayi fom | Hoto: Gbenga Olawepo-Hashim
Asali: UGC

Ya dage cewa duk da cewa kasar a halin yanzu Najeriya na durkushe cikin tsananin rashin isassun kayayyakin aiki saboda wasu dalilai, ya ce yayi imanin cewa zai kawo sauyi a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa, hankalin siyasar yanzu ya lura ya karkata ne ga kabilanci, wanda ke kawo cikas ga zaman lafiya da rashin jituwa.

A bangarensa, ya yi alkawarin kawo sauye-sauye da dama a kasar nan, inda yace yana kalubalantar yadda ake tafiyar da kasar na tsawon shekaru.

Ya yi alkawarin dinke barakar da ake samu a cikin al’umma, zai warkar da raunuka, ya dawo da al’umma baki daya kan turba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

“Saboda wani dalili, mahaifina ya fito daga Arewacin Najeriya, mahaifiyata kuma daga Kudu. Rabin dangina Kiristoci ne yayin da sauran rabin kuma Musulmai ne.
“Na zauna kuma na yi karatu a Arewa da Kudu da kuma Turai da Amurka. Na san cewa dukkan ’yan Adam an haife su daidai ne kuma sun cancanci daidaitattun hakkoki, dama da adalci.
“Zan yi adalci ga kowa ba tare da nuna wariya ba saboda kabilanci, addini da jinsi. Wannan ba holokon alkawari ba ne na wani dan siyasa. Ni ne, haka kuma nake.”

Wani Ministan Buhari zai ayyana shirin takarar Shugaban kasa nan da awanni 48

A wani labarin, Godswill Akpabio wanda yake rike da kujerar Ministan Neja Delta zai fito takarar shugaban kasa a ranar Laraba, 4 ga watan Mayu 2022.

Anietie Ekong wanda yake magana da yawun bakin Sanata Godswill Akpabio ya shaidawa manema labarai wannan. The Cable ta fitar da rahoton.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Da aka zanta da Hadimin Ministan a ranar Litinin, ya tabbatar da cewa mai gidansa zai yi takara.

Kamar yadda Ekong ya shaidawa ‘yan jarida, labarin da ke yawo a game da takarar Ministan ba karya ba ne, zai ayyana takararsa a tsakiyar makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel