Hotuna: Malami Ya Gwangwaje 'Sojojin Baka' Da Motoccin Alfarma Irinsu Mercedes Benz, Prado Da Lexus a Kebbi
- Mr Abubakar Malami (SAN) Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa ya yi rabon motoccin alfarma ga sojojin baka da mukarrabansa a Kebbi
- Cikin motocci guda 26 da Malami ya rabar akwai Mercedes Benz GLK guda 14 Lexus LX570 guda 4 da kuma Prado SUV da Hilux guda 8
- Daya daga cikin wadanda suka amfana da kyautan motoccin ya bayyana cewa Malami ya basu kyautan ne a matsayin tukwici gabanin kaddamar da takararsa na gwamnan Kebbi
Ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami (SAN) ya gwangwaje sojojin baka da kugiyoyin magoya bayansa da wasu mukarrabansa da motoccin alfarma.
Daya daga cikin wadanda suka samu kyautan motoccin wanda ya yi magana da Daily Nigerian ya ce ministan ya musu kyautan ne a matsayin tukwici gabanin kaddamar da takararsa na gwamnan Jihar Kebbi a 2023.
Daily Nigerian ta tattaro cewa ministan ya bada Mercedes Benz GLK guda 14 ga sojojin baka wadanda ke tallata shi da kare takararsa na gwamna.
Wasu na kusa da ministan su kuma sun samu kyautan Lexus LX 570 su hudu.
Mutum takwas sun samu kyuatan Prado SUV sai Toyota Hilux guda hudu ga kungiyoyin goyon baya da gidauniya na Malami; Khadimiyya Foundation, Khadi Malami Foundation, Malami Drum Beats, Malami Women Support Organisation da Aisha Malami Centre for Women Development da matarsa ke goyon baya.
Ga hotunan motoccin a kasa:
Tamkar Takwararsa na Zamfara, Gwamnan Bauchi Shi Ma Ya Yi Wa Masu Sarautan Gargajiya Rabon Motoccin Alfarma
A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya raba wa hakimai da shugabannin kananan hukumomi 20 a jiharsa motoccin alfarma guda 28 kamar yadda The Punch ta rahoto.
Gwamnan ya bada motoccin 38 ne ga hakimai da ke masarautu shida da ke jihara yayin da kowanne shugaban karamar hukuma cikin kananan hukumomi 20 ya samu mota daya.
Ma'aikatar kananan hukumomi ta samu Toyota Hilux guda biyu yayin da suma ofishoshin kananan hukumomi suka samu Toyota Hilux guda shida.
Asali: Legit.ng