Tamkar Takwararsa na Zamfara, Gwamnan Bauchi Shi Ma Ya Yi Wa Masu Sarautan Gargajiya Rabon Motoccin Alfarma
- Sanata Bala Mohammed, gwamnan Jihar Bauchi ya yi wa hakimai da shugabannin kananan hukumomi rabon motocci
- Gwamna Bala ya ce wannan rabon ta biyo bayan bukatar da mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwan Suleiman ya yi ne a bara
- Sanata Bala Mohammed ya ce hakiman da shugabannin kananan hukumomin suna aiki tukuru don hakan wannan tukwici ne a gare su
Jihar Bauchi - Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya raba wa hakimai da shugabannin kananan hukumomi 20 a jiharsa motoccin alfarma guda 28 kamar yadda The Punch ta rahoto.
Gwamnan ya bada motoccin 38 ne ga hakimai da ke masarautu shida da ke jihara yayin da kowanne shugaban karamar hukuma cikin kananan hukumomi 20 ya samu mota daya.
Ma'aikatar kananan hukumomi ta samu Toyota Hilux guda biyu yayin da suma ofishoshin kananan hukumomi suka samu Toyota Hilux guda shida.
An raba wa hakimai motoccin ne a matsayin tukwici bisa ayyukan da suke yi, Bala Mohammed
Da ya je jawabi a wurin taron rabon motoccin, gwamnan ya ce wannan karamcin amsa ce ga rokon da Sarkin Bauchi, Rilwan Suleiman ya yi a bara, na gwamnatin ta taimakawa hakimai da motocci don inganta ayyukansu, LatestNews ta rahoto.
"Yau ba ranar yin jawabi bane amma ranar amsa bukatar mai girma Sarkin Bauchi. Zan iya tunawa shekara guda da ta gabata lokacin hutun Ramadan, ya bukaci mu duba yiwuwar samar wa hakiman da suke aiki da shi motocci, a Bauchi. A madadin gwamnati da mutanen Bauchi, na yi alkawari, na gode wa Allah cewa yau muna cika alkawarin.
Hotunan Motoccin Alfarma Da Matawalle Ya Siya Wa Masu Sarautun Gargajiya 260 a Zamfara Ciki Har Da 'Cadillac'
"Kuma, shugabannin kananan hukumomin mu, mun san suna aiki tukuru kuma tunda aka zabe su ba a basu motocci ba kamar yan majalisa da sauran zababbu. Don haka, mun yanke shawarar suma su amfana da bukatar mai martaba. Gwamnatin Jiha a siyo musu motocci matsayin tukwici bisa ayyukan da suke yi," in ji shi.
Hotunan Motoccin Alfarma Da Matawalle Ya Siya Wa Masu Sarautun Gargajiya 260 a Zamfara Ciki Har Da 'Cadillac'
Tunda farko, Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed ya raba wa shugabannin gargajiyan jiharsa motoci 260 sannan ya kaddamar da hedkwatoci na zamani ga kungiyar malaman jihar, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Daga rabon har kaddamarwar duk Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar 111 ne ya gabatar da su a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Laraba, rahoton Daily Trust.
Sarkin Musulmin ya nuna farin cikinsa kana ya mika godiyarsa ga Gwamna Matawalle akan yadda ya damu da walwalar shugabannin gargajiya, wanda a cewarsa hakan ne zai tabbatar da hadin kan al’umma.
Asali: Legit.ng