Jam'iyyar PDP ta lashe kujerun Ciyaman 23 da Kansiloli 276 a jihar Benuwai

Jam'iyyar PDP ta lashe kujerun Ciyaman 23 da Kansiloli 276 a jihar Benuwai

  • Jam'iyyar PDP ta yi nasarar lashe dukkan kujeru a zaɓen kananan hukumomin jihar Benuwai da aka gudanar ranar Asabar
  • Shugaban hukumar zaɓe ta jihar, Tersoo Loko, yayin sanar da sakamakon ranar Lahadi, ya ce PDP ta lashe ciyaman 23 da Kansiloli 276
  • Kwamandan hukumar NSCDC na jihar ya ce hukumrsa ta tura jami'ai lungu da sakon jihar don tabbatar da tsaro a zaɓen

Benue - Jam'iyyar People Democaratic Party (PDP) ta sami nasarar lashe dukkan kujerun da aka kaɗa kuri'a kan su a zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar a Benuwai ranar Asabar.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Benuwai, ita ce ta bayyana sakamakon zaɓen ranar Lahadi a Makurɗi, babban birnin jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Tersoo Loko, yayin da yake bayyana waɗan da suka samu nasara, ya ce PDP ta lashe kujerun Ciyamomi 23 da Kansiloli 276 a zaɓen wanda aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP ta lashe kujerun Ciyaman 23 da Kansiloli 276 a jihar Benuwai Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce jam'iyyun siyasa hudu ne suka shiga aka fafata da su a zaɓen, waɗan da suka haɗa da AAC, PDP, APGA, Labour Party (LP) da SDP, kamar yadda Punch ta tattaro.

Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ba ta shiga zaɓen ba domin tun farko masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Benuwai sun roki mambobin APC su kauracewa zaɓen.

Haka nan, Loko ya tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin inganci, sahihanci ba tare da samun hayaniya ba a faɗin kananan hukumomin jihar.

Hukumar NSCDC ta ba da tsaro a zaɓen

Tun da farko, hukumar Civil Defence reshen jihar Benuwai ta bayyana cewa ta jibge jami'anta 1,250 a dukkan sassan jihar domin ba da tsaro kafin da lokacin zaɓen.

Kwamandan NSCDC, Phillip Okoh, ya ce hukumarsa ta san halin da ake ciki game da tsaro, amma dakarunsa. ba zasu bar ko kofa ɗaya ba wajen tsare dukiya da rayukan al'umma.

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

A wani labarin kuma Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto ranar Lahadi

Wasu al'umma mabiya Addinin Musulunci a Sokoto sun gudanar da Sallar Eid-El-Fitr yau Lahadi inda suka saba wa umarnin Sarkin Musulmai.

Mutanen waɗan da mafi yawancin su mabiya Shekih Musa Lukwa ne, sun yi Sallah da misalim ƙarfe 8:00 na safe bayan tabbatar da ganin wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel