2023: PDP ta soke 6 daga cikin yan takararta na sanata a jihar Kogi
- Kwamitin tantance yan takara na PDP ya soke takarar wasu masu neman kujerar sanata a jihar Kogi guda shida
- An ajiye wasu daga cikin yan takarar ne saboda manyan zarge-zarge da ake masu na yiwa jam’iyya rashin da’a
- Sai dai akwai yiwuwar yan takarar su daukaka kara kan hukuncin kwamitin ta hanyar zuwa kotu kan lamarin
Jihar Kogi – Rahotanni sun kawo cewa kwamitin tantance yan takara na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya soke takarar wasu masu neman kujerar sanata guda shida a jihar Kogi.
Daga cikin wadanda aka soke takarar tasu a ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, harda Ubolo Itodo Okpanachi da Aminu Abubakar Suleiman wadanda ke neman kujerar sanata mai wakiltan Kogi ta gabas kan zarginsu da ake da aikata rashin da’a.
Sakamakon shirin tantancewar ya nuna cewa yayin da Isaac Alfa da Victor Adoji suka samu yardar kwamitin domin ci gaba da takararsu, an soke takarar Suleiman da Okpanachi.
Kwamitin tantance yan takarar a Lokaja ya bayyana cewa an soke takarar Suleiman ne saboda bai da rijista a yankin, don haka ba zai iya shiga zaben sanatan ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani siga da aka yi amfani da shi wajen fitar da Suleiman shi ne cewa bai zabi kowa ba a Kogi ta Gabas, Nigerian Tribune ta rahoto.
An zargi Okpanachi da zama dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda ake zargin ya samu mukami.
Hakazalika an soke takarar hudu daga cikin yan takara bakwai da ke neman kujerar sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya ciki harda na tsohon sanata, Ahmed Ogembe.
An kuma soke takarar Ismail Inah Hussein mai neman kujerar dan majalisar wakilai daga mazabar Idah kan hujjar aikata abun da ya sabawa jam’iyya.
Sai dai kuma, yan takarar da aka soke takararsu sun nuna ra’ayin tunkarar kwamitin daukaka kara na jam’iyyar domin kalubalantar hukuncin kwamitin tantance yan takarar, PM News ta rahoto.
Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta bashi dama a zaben fidda dan takararta na shugaban kasa saboda shine dan takara mafi cancanta da zai kawo mata kujerar.
Da yake jawabi ga mambobin kwamitin NWC na jam’iyyar a ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, Atiku ya ce ya kamata a yi la'akari da shi saboda tuni ya mallaki kuri’u miliyan 11 da ke jiransa, Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng