Ana tsaka da ruwan sama, ana tantance Atiku, Saraki da sauran yan takara a PDP

Ana tsaka da ruwan sama, ana tantance Atiku, Saraki da sauran yan takara a PDP

  • Duk da ruwan saman da aka sharara a birnin Abuja, an fara zaman tantance yan takaran kujeran shugaban kasa na PDP
  • Kawo yanzu an tantance tsohon dan takara, Alhaji Atiku Abubakar, Sanata Bukola Saraki da Sanata Pius Anyim
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ke jagorantar kwamitin tantancewar

Abuja - Ana tsaka da ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin tarayya Abuja, ana tantance masu neman takarar kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Wannan tantancewa na gudana a Legacy House, sabanin Wadata House hedkwatar jam'iyyar ta kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

Tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa lallai an tantancesa duk da ruwan saman da ake yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yau masu harin kujerar Shugaban kasa a PDP za su san matsayin takararsu

Atiku yace:

"Ko ruwan sama da ake yi bai hana ni zuwa tantancewa gaban kwamitin David Mark ba."

Atiku
Ana tsaka da ruwan sama, ana tantance Atiku, Saraki da sauran yan takara a PDP Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Punch ta ruwaito cewa an fara tantancewar ne misalin karfe 11 na safe kuma kawo yanzu an tantance mutum uku.

Sun hada da tsohon mataimakin shugaban kaa, Atiku Abubakar; tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim.

Jerin yan takaran shugaban kasa karkashin PDP 17 da ake tantancewa yau

Mutum 17 ne suka sayi Fom din takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Cikinsu akwai maza 16 da mace 1.

Duba jerinsu a nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel