An buga an bar ka: Abin da ya sa aka gagara tsige ni daga shugaban majalisa - Bukola Saraki

An buga an bar ka: Abin da ya sa aka gagara tsige ni daga shugaban majalisa - Bukola Saraki

  • Bukola Saraki ya kai ziyara zuwa Kuros Riba domin samun goyon bayan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP
  • Saraki ya ce ya hada-kan Sanatoci da ya ke rike da kujerar shugaban majalisar dattawan Najeriya
  • Tsohon shugaban majalisar kasar ya yi alkawarin zai tafi da matasa, ya nema masu hanyoyin samu

Calabar - Tsohon shugaban majalisar dattawan na Najeriya, Bukola Saraki ya yi bayanin abin da ya sa ya kammala wa’adinsa ba tare da an tunbuke shi ba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Bukola Saraki ya bada labarin irin barazanar da yake fuskanta daga gwamnati mai-ci a lokacin yana rike da majalisar dattawa.

Mai neman takarar shugaban kasar ya zauna da ‘ya ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP a Transcorp Hotel a Kalaba domin samun kuri’arsu a zaben tsaida gwani.

A cewar Saraki, ya hada kan ‘yan majalisa, hakan ya sa tunbuke shi daga mukaminsa ya yi wahala. A lokacinsa ya yi ta fama da shari'a a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Abin da ya fadawa ‘yan jam’iyyar hamayya

“Na rike mutane da kyau har ta kai zai yi wahala ga wadanda suke adawa da ni su tsige ni daga ofis.”
“Ina da kyakkyawar alaka da mutane ne. Ina maganar duk wanda ya kamata ayi la’akari da shi a majalisa.”
Tsohon shugaban majalisa
Bukola Saraki a Kalaba Hoto: @bukola.saraki
Asali: Facebook
“Na hada kan jama’a. Mu na bukatar shugaban kasa da zai iya hada kan kowa. Ni mutum ne da idan aka daura ni a kujera, zan kawo gyara kafin in tafi.”

- Bukola Saraki

Shugaban da ake bukata a 2023

Vanguard rahoto tsohon gwamnan na Kwara yana cewa kafin mutum ya yi nasara a matsayin shugaban kasa, dole ya zama mai tunani da kuma hangen nesa.

Saraki ya ce ana bukatar wanda zai iya tunanin yadda biyar za ta zama goma a matsayin shugaba. Hakan sai da karatu, shaidar ilmi da sanin kasuwanci.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

Alkawarin damawa da matasa

“Dole mu tafi da matasa a gwamnatinmu. Tilas ne matasa su zama Ministoci a gwamnatina.”
“Ina neman goyon bayanku. Zan cika alkawarin da na dauka. Ni da mutanen da zan dauko mu yi aiki da su a gwamnatina, za mu gyara kasar nan.”

- Bukola Saraki

Sanatoci su na neman mulki

A jiya ku ka ji cewa an samu wasu ‘Yan majalisar dattawa akalla uku zuwa yanzu daga kudancin Najeriya da suke shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Baya ga wadannan akwai wasu tsofaffin Sanatocin da za su shiga neman shugabanci. A cikinsu ne ake da Bukola Saraki, Rabiu Kwankwaso da su Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng