2023: Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m

2023: Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m

  • Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Dimeji Bankole, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023
  • Wani makusancin Bankole ya tabbatar da cewa Uban gidansa ya fara shirye-shirye, kuma zai karɓi Fom mako mai zuwa
  • Tuni dai wasu rahotanni suka bayyana cewa tsohon kakakin ya fara neman goyon bayan manyan masu ruwa da tsaki

Abuja - Tsohon kakakin majalisar wakilai, Honorabul Dimeji Bankole, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Bankole ya shirya lale miliyan N100m domin sayen Fom karkashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress wato APC.

Wani makusancin tsohon kakakin majalisar wakilan, Malam Abdullahi Bayero, shi ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ranar Laraba.

Tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole.
2023: Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Malam Bayero ya ce:

Kara karanta wannan

Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano

"Honorabul Dimeji Bankole ya shiga tseren kuma yana neman takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar APC. Ya gana da masu ruwa da tsaki kuma ya samu goyon baya, musamman a Arewa."
"Saboda haka ya shirya Sayen Fom mako mai zuwa. Da yawan mutane na ganinsa a matsayin wanda ya cancanta ta kowane ɓangare, matashi, mai kwanya."
"Kamar yadda tsohon shugaban ƙasa na mulkin Soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya faɗa, Najeriya na bukatar matashin shugaba, babu tantama kan haka duk da kwansutushin be dakatar da tsaffi ba."

Ya fara neman goyon baya

A kwanaki kaɗan da suka shuɗe, Bankole ya ziyarci Kaduna a matsayin babban bako a wurin Lakcan watan Ramadan karo na 16, wanda kafafen NTA, FRCN da VOA ke shiryawa.

Bayanai sun nuna cewa tsohon kakakin ya yi amfani da wannan dama wajen ganawa da manyan masu ruwa da tsaki, kuma sun nuna masa goyon baya.

Bankole wanda ya nemi takarar gwamnan jihar Ogun a zaɓen 2019 karkashin jam'iyyar ADP, ya yi rijista da APC a hukumance cikin watan Maris, 2021.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamna ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo, ya umarci a damƙe shi

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo kan abu ɗaya

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya umarci a kama ɗan majalisar tarayya, Farah Dagogo ko ina ya shiga.

Wike ya dauki wannan matakin ne bisa zargin ɗan majalisar ya tura yan daba Sakariyar PDP dake Patakwal su ta da yamutsi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262