Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano

Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano

  • Tsohon Janar din Soja ya gudu hannun jami'an hukumar rashawa yayinda aka fara bincikensa
  • Hukumar ta gayyacesa yi masa tambayoyi ofishintabisa zargin yin ba dai-dai ba da aka yi masa

Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano (PCACC) ya bayyana cewa Janar Idris Bello Dambazau (mai ritaya), Diraktan hukumar kare hakkin masu siyayya, ya gudu daga hannunta.

Mukaddasin shugaban hukumar PCACC, Barista Mahmoud Balarabe, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba.

A bisa rahoton Daily Trust, Balarabe ya ce suna cikin yiwa Dambazau tambayoyi a hedkwatar hukumar ranar Talata sai ya bukaci zuwa gida shan magani.

Balarabe yace an jami'an hukumar suka raka shi gida amma kafin su ankara yayi layar zana.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

Ya ce tuni suna gayyatar Dambazau amma ya ki zuwa sai ranar Talata bayan sun yi barazanar damkeshi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Balarabe ya kara da cewa sun gayyacesa ne bisa zargin rashawa da ake masa.

Janar Idris Dambazau
Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano
Asali: Facebook

A ranar Alhamis, Hukumar Korafin Jama’a da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta yi barazanar kama shugaban Hukumar Kare Hakkin Kwastomomi ta Kano, KCPC, Idris Bello Dambazau.

Hakan ya biyo bayan yadda Dambazau, wanda soja ne mai murabus, ya ki amsa gayyatar da hukumar ta yi masa na zarginsa da aikata wasu laifuka tare da rashawa kamar yadda shugaban PCACC, Mahmoud Balarabe ya shaida.

Balarabe ya ci gaba da cewa, akwai korafi da dama na zargin rashawa da wasu laifuka da aka tura musu akan shugaban KCPC din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel