‘Dan Jam’iyya ya rubutawa Shugabannin APC takarda, yana so a hana Gwamna tazarce
- Ayodele Oludiran ya aika korafi a kan gwamnan jihar Ogun a lokacin da ake daf da zaben gwani
- A korafin da ya gabatar, ‘dan jam’iyyar yana cewa Dapo Abiodun ya taba aikata laifi a kasar waje
- Bayan batun boye wancan laifin, ana zargin Gwamnan na Ogun da ya yi wa hukumar zabe karya
Ogun - Ayodele Oludiran wanda yana cikin ‘yan jam’iyyar APC a jihar Ogun, ya kai karar gwamnansa wajen shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu.
Daily Trust ta ce Ayodele Oludiran ya gabatar da korafinsa gaban Sanata Abdullahi Adamu, yana mai jan kunnensa a kan sake ba Gwamna Dapo Abiodun takara.
A cewar Oludiran, zargin da suke kan gwamnan ya sa akwai hadari a ba shi tutar APC a 2023.
Rahoton ya tabbatar da cewa takardar korafin ‘dan jam’iyyar ta shiga sakatariyar APC na reshen jihar Ogun da ke garin Abeokuta ranar 12 ga watan Afrilu 2023.
Zargin da ake yi wa Abiodun
Mai korafin ya ke cewa gwamna Dapo Abiodun ya taba yin rufa-rufa kan wani babban laifi da ya aikata a kasar Amurka shekaru kimanin 40 kenan da suka wuce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, Ayodele Oludiran yana ikirarin akwai bambanci a takardun shiga takarar da Mai girma gwamnan ya gabatarwa hukumar INEC a 2015 da 2019.
A lokacin da ya shiga takara a zaben 2015, Oludiran ya ce Abiodun ya yi ikirarin halartar hami’ar Ife watau OAU a shekarar 1986, daga baya kuma ya canza magana.
Da ya gabatar da fam dinsa na CF001 da zai nemi takara a 2019, Abiodun bai ambaci inda ya yi karatun jami’a ba. Hakan ya jawo ake zargi akwai abin da aka boye.
Magana ta je gaban NWC
Ambasada Samuel Jimba ya tabbatar da cewa uwar jam’iyya ta karbi wannan takarda. Amma an samu wasu lauyoyi da suke kokarin wanke gwamna Abiodun daga zargi.
Premium Times tace Afe Babalola & Co sun bukaci Abdullahi Adamu da ‘yan majalisarsa su yi watsi da korafin da aka gabatar domin bai da wani tushe ko makama.
Lauyoyin sun ce ba zai yiwu ayi amfani da abin da ke cikin fam din da aka yi amfani da su a zabukan 2015 da 2019 wajen hana gwamnan neman takara a badi ba.
Fayemi zai nemi takara?
A makon nan aka ji Gwamnan Ekiti Kayode John Fayemi ya na cewa irinsa ake nema a Aso Villa a 2023; wanda ya san kan aiki, yake da ilmi, kuma maras tsoron komai.
Shugaban gwamnonin Najeriyan ya ce mukaman da ya rike a gwamnati sun sa ya dace ya cigaba daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya domin kai kasar ga ci.
Asali: Legit.ng