2023: Abinda shugaba Buhari ya faɗa mun kafin na ayyana shiga takarar shugaban ƙasa, Gwamna Ayade
- Gwamna Ayade na jihar Kuros Riba ya ce shugaban ƙasa Buhari ne ya ba shi shawarar ya fito takara a fafata da shi
- Gwamnan wanda ya gana da Buhari kafin ayyana shiga takara, ya bayyana abinda suka tattauna da shugaban ƙasa
- Sai dai Ben Ayade ya ce a shirye yake ya janye wa duk ɗan takarar da Buhari ya nuna goyon baya a kansa
Abuja - Gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade, ya shiga jerin yan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC a hukumance.
Ayade, wanda ya gana da shugaba Buhari ranar Talata, ya ce bai taɓa tunanin shiga takara ba har sai lokacin da Buhari ya buƙace shi da ya shiga.
Gwamnan ya faɗa wa manema labarai haka jim kaɗan bayan fitowa daga wurin ganawa da shugaban ƙasa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Ayade ya ce ya je fadar shugaban ƙasa ne domin neman haske daga Buhari kan yadda ya dace ya tafiyar da harkokin siyasarsa na gaba, amma Buhari ya umarce shi ya shiga takara.
Me shugaba Buhari ya faɗa masa?
A cewar gwamna Ayade, shugaba Buhari ya faɗa masa cewa:
"Kai gwamna ne daga yankin kudu maso kudu, kawai ka shiga kai ma kuma ka nemi shawari."
"Na ji daɗi da kazo nan dan ka shaida mun zaka tsaya takara bane, ka zo ne ka goyi baya na. Zan sa ido na ga rawar da zaka taka idan ka fita can."
Wace manufa ya sa a gaba game da takara?
Ayade ya bayyana kansa a matsayin tsayayyen ɗan takara, duk da a kowane lokaci a shirye yake ya koma bayan duk wanda shugaba Buhari ke so.
"Zan mara wa ɗan takarar da shugaban ke so, duk da cewa zan kasance a shirye, idan kaine zabin, zan goyi bayan wanda Buhari yake goyon baya."
A wani labarin kuma Sanata Orji Kalu na APC ya ce bai janye daga takarar shugaban ƙasa ba kuma ba zai taba janye wa ba
Sanata Orji Kalu ya musanta raɗe-raɗin dake yawo cewa ya janye daga takarar shugabam ƙasa karkashin APC a zaɓen 2023.
Sanatan ya ce yana nan daram kan bakarsa ta neman kujera lamba ɗaya, kuma ba zai taɓa janye wa ba
Asali: Legit.ng