2023: Mutumin da Shugaba Buhari ke son ya gaje shi zai ba kowa mamaki, Okorocha

2023: Mutumin da Shugaba Buhari ke son ya gaje shi zai ba kowa mamaki, Okorocha

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya ce shugaba Buhari ka iya ba kowa mamaki gme da ɗan takara
  • Sanatan, wanda ke ɗaya daga cikin masu hangen kujera lamba ɗaya, ya ce shugaba Buhari yana da matukar wayo
  • A cewarsa, kafin Buhari ya zaɓi wanda yake son APC ta baiwa takara sai ya yi nazari sosai da neman shawari

Abuja - Sanata Rochas Okorocha na jihar Imo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya zarce tunanin duk wani mai hasashe.

Sanatan ya ce Buhari ka iya ba kowa mamaki game da ɗan takarar da zai goyi baya karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen dake tafe.

Rochas Okorocha, wanda ya kwashe wa'adin mulki biyu a matsayin gwamnan Imo, ya yi wannan furucin ne a shirin 'Siyasa a yau' na gidan Talabijin Channels tv.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen gwamnoni a APC, PDP da suka shirya janye wa Jonathan takara a 2023

Sanata Rochas Okorocha.
2023: Mutumin da Shugaba Buhari ke son ya gaje shi zai ba kowa mamaki, Okorocha Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na ɗaya daga cikin yan takarar dake fafutukar samun tikitin jam'iyyar APC a yunkurinsa na gaje Buhari a 2023, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan ya ce ka iya yuwuwa shugaba Buhari yana da wanda ya ke so a cikin yan takarar nan, amma ya rike a zuciyarsa ya ƙi faɗawa duniya.

Wane ɗan takara Buhari zai zaɓa?

Ya ƙara da cewa Buhari zai zaɓi wanda zai gaje shi ne bayan duba abubuwa kamar yanayin da ƙasa ke ciki, abin da mutane ke so, APC, da dai sauran su.

Okorocha ya ce:

"Idan kasan shugaban kasa Buhari, shi janar ne kuma ya zarce hasashe, ba zaka iya cinkar abinda zai yi ba. Zai iya jefa kowa cikin mamaki."
"Buhari yana da Basira, zai duba muhimman abubuwa kafin ya yi zaɓinsa, zai duba yanayin ƙasa ya ga waye zai iya tafiyar da ita; wanda zai iya kai APC ga nasara, domin gaskiya ba ya son PDP ta koma mulki."

Kara karanta wannan

Abubuwan da shugaba Buhari ya faɗa mun har na ayyana shiga takarar shugaban ƙasa, Gwamnan APC

"Saboda haka zai zauna ya yi nazari da kwakwalwarsa ya gani, wannan mutumin zai iya, wannan kuma ba zai iya ba, Buhari zai nemi shawari."

A wani labarin kuma Wasu masoyan shugaba Buhari sun koma bayan Kwankwaso ya gaji shugaban ƙasa a 2023

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na gaje Buhari a 2023.

Wata ƙungiyar yan a mutun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta tabbatar da goyon bayanta ga jagoran Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel