Mai ba Buhari shawara ya lale Naira miliyan 50, ya saye fam din Gwamna a tashin farko

Mai ba Buhari shawara ya lale Naira miliyan 50, ya saye fam din Gwamna a tashin farko

  • Daga bude saida fam sai aka ji Ita Enang ya biya N50m domin shiga takarar gwamna a karkashin APC
  • Hadimin na shugaba Muhammadu Buhari zai nemi takarar gwamna a jihar Akwa Ibom a zaben 2023
  • Sanata Ita Enang ya koma jiharsa ne ta Akwa Ibom, ya dauko burin gaje kujerar Emmanuel Udom a Uyo

Abuja - Mai taimakawa shugaban kasa wajen harkokin Neja-Delta, Ita Enang ya bada sanarwar sayen fam din takarar kujerar gwamna a zaben 2023.

Sanata Ita Enang wanda shi ne babban mai ba Muhammadu Buhari shawara a kan abin da ya shafi sha’anin Neja-Delta zai nemi takara a jam’iyyar APC.

Da yake magana a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu 2022, Ita Enang ya tabbatar da cewa ya kashe N50m wajen yankan fam.

Kara karanta wannan

Bayan ya gana da Buhari, ‘Dan takara ya fadi matsayarsa a kan tsaida Jonathan a 2023

‘Dan siyasar mai shekara 59 yana cikin wadanda suka yi maza su ka saye fam bayan APC mai mulki ta bude kafar saidawa ga masu neman mukamai.

Tsohon Sanatan ya ce tun da safiyar Talatar nan ya tura kudin cikin asusun da jam’iyya ta bada.

“Ya ku ‘yan jam’iyya, jagorori da masu son kawo cigaba, da kimanin karfe 9:30 na safen yau (Talata), na tura N50m cikin asusun da APC ta bada domin sayen fam na neman shiga zaben gwamna (N40m) da na sha’awar kujera (N10m), domin sayen fam din takarar gwamnan JIHAR AKWA IBOM.”
“Ina rokon sa’ar Ubangiji a wannan tafiya da za mu yi. Da taimakon Allah, da gudumuwarku, za mu yi dace.”

- Ita Enang

Siyasar Ita Enang

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

Kafin yanzu, Ita Enang ya taba wakiltar mutanen Itu da Ibiono na jihar Akwa Ibom a majalisar wakilan tarayya na shekaru 12 tun daga 1999 zuwa 2011.

A shekarar 2011 ne Enang ya yi nasarar zama Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas a majalisar dattawa, a shekarar 2015 ya bar majalisa.

Bayan nan sai shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin hadimi a harkar majalisa. Daga baya ya koma bada shawara a kan sha’anin Neja Delta.

Enang zai so ya zama magajin Emmanuel Udom wanda yake mulki a karkashin jam’iyyar PDP a Akwa Ibom. Wa’adin gwamnan zai kare a shekara mai zuwa.

Ahmaad zai nemi Majalisa

A makon da ya gabata, an ji cewa Bashir Ahmaad ya tabbatar da shirin fitowa takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a jihar Kano a jam'iyyar APC.

Shi ma Hadimin shugaban kasar yana so ya wakilci mutanensa na mazabar Gaya, Ajingi da Albasu a zaben 2023 idan har ya yi nasarar samun tikiti.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng