Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC
- Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Kasa, Felix Morka ya dage cewa farashin fom kan N100m na Jam’iyyar ga 'yan takarar Shugaban kasa bai yi tsada ba
- A cewar Morka, ikon dan takara na tara kudi wani ma'auni ne bayyananne na nuna cancantar shiga tsaren takaran shugaban kasa
- Ku tuna cewa APC ta kayyade farashin Naira miliyan 100 na nuna sha'awa da sayen fom din takarar shugaba a zaben mai zuwa
Najeriya - Felix Morka, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, ya ce duk wanda ke da muradin zama shugaban kasa to ya samu “isasshen tushe” da zai tara Naira miliyan 100 na sayen fom din takara.
Ya fadi haka ne a ranar litinin da ta gabata lokacin da aka yi hira da shi a wani shiri na gidan talabijin na Silverbird, The Cable ta ruwaito.
Jam’iyyar APC ta kayyade farashin fom din takarar shugaban kasa kan kudi Naira miliyan 100 ga masu sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Legit.ng Hausa ta tattaro yadda 'yan Najeriya suka kadu, suke ta cece-kuce game da wannan shawara ta jam'iyyar mai mulki.
Da yake magana game da kudaden fom din, Morka ya ce duk da cewa ana ganin farashin ya yi yawa idan aka yi la'akari da yanayin Najeriya, masu fatan tsayawa takarar shugaban kasa ya kamata su sami tallafin da ya dace don tara irin wannan adadin kudi.
Ya kuma bayyana cewa, ko a Amurka dan siyasar da ke da burin tsayawa takara dole ya nemo tallafai, sannan dole ya fadi manufofinsa domin neman jama'a su tallafa masa.
A cewarsa:
“A halin da ake ciki a Najeriya, Naira miliyan 100 kudi ne mai yawa. Masu neman mukami a fadin kasar nan ana sa ran samun isasshiyar tushen kudi, in ba haka ba, me ya sa za ku yi burin zama shugaban kasa, idan kuna cikin duhu ko rashin goyon bayan 'yan jam'iyyarku da masu zabe?"
Osinbajo ya yi karin-haske kan dalilin yin takara, yace akwai sirrin da shi kadai ya sani
A wani labarin, mai girma mataimakin shugaban kasa yana ganin cewa rashin adalci ne ya ki neman takarar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.
Daily Trust ta ce Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu 2022 da ya kai ziyara ta musamman zuwa jihar Ondo.
Farfesa Osinbajo ya na ganin ya samu gogewar da zai rike gwamnatin Najeriya ganin yadda ya shafe shekaru har bakwai yana aiki a fadar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng