Osinbajo ya yi karin-haske kan dalilin yin takara, yace akwai sirrin da shi kadai ya sani
- Mataimakin shugaban Najeriya ya kai wa Gwamna Rotimi Akeredolu ziyara har gidan gwamnati
- Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa cin amana ne ya ki fitowa takarar shugaban kasa a 2023
- Osinbajo ya ce damar da ya samu a shekaru bakwai da ya yi a Aso Villa ta sa ya samu kwarewa
Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa yana ganin cewa rashin adalci ne ya ki neman takarar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.
Daily Trust ta ce Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu 2022 da ya kai ziyara ta musamman zuwa jihar Ondo.
Farfesa Osinbajo ya na ganin ya samu gogewar da zai rike gwamnatin Najeriya ganin yadda ya shafe shekaru har bakwai yana aiki a fadar shugaban kasa.
'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo
Yemi Osinbajo ya jinjinawa Maigidansa watau Muhammadu Buhari saboda damammakin da ya rika ba shi, ya daura masa nauyin wasu muhimman ayyuka.
Osinbajo yake cewa ya san Ubangiji ne yake ba ‘Dan Adam mulki, amma duk da haka tamkar cin amana ne a ce ya yi ritaya ba tare da ya nemi shugabanci ba.
Kamar yadda Vanguard ta fitar da rahoto, Osinbajo yana ganin an yi asara idan duk kwarewar da ya samu a gwamnatin tarayya suka tafi a banza bayan 2023.
Jawabin Osinbajo a Akure
“Shugaba Muhammadu Buhari saboda irin alherinsa ya tabbatar cewa an ba ni muhimman ayyuka a matsayina na mataimakin shugaban kasa.”
“Sannan kuma na rike kujerar shugaban kasa na rikon kwarya. A wadannan kujeru, na fahimci abubuwan da mutane da-dama ba za su taba sani ba.”
Ina da kwarin guiwa da izinin Allah wannan ɗan takarar ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan Kano ya magantu
“Na san abubuwan da har wadanda ke cikin gwamnati ba za su taba sani ba. Bayan nan, na samu karin kwarewa da sanin aiki sosai a dalilin wannan.”
“Ina tunanin cin amanar kasarmu ne, duk abin da na samu da ikon Allah, sai in ce zan koma garin Legas ko Ikene, in boye ina rubuta littatafan tarihina.”
- Yemi Osinbajo
Akeredolu ya ji dadin ziyara
A kan wannan, mataimakin shugaban kasar ya ce ya fito takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Mataimakin shugaban kasar ya gana da Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu a ofishinsa a Akure. Gwamnan ya nuna ya ji dadin wannan ziyara da aka kawo masa.
Buhari zai raba gardama
An ji labari cewa a watan Mayun 2022 ne shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana wanda yake goyon bayan ya samu takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar APC.
Kamar yadda shugaban kasa ya shiga maganar zaben shugabannin APC na kasa, haka zai yi ya raba fada tsakanin Bola Tinubu da su Yemi Osinbajo da ke neman tikiti.
Asali: Legit.ng