An yanka ta tashi a PDP bayan Dattawan Arewa sun ce ba su tsaida Bala da Saraki ba
- Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta NEF ta bayyana matsayarta a kan batun maslaha a PDP
- NEF ta ce Farfesa Ango Abdullahi ne wanda ya jagoranci wannan aiki ba Kungiyar Dattawan ba
- Hakeem Baba-Ahmed ya shaida cewa ra’ayin kungiyar ita ce a bar ‘yan jam’iyya da harkar zabensu
Abuja – Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, ta nesanta kanta daga rahoton da ke cewa ta zabi Bala Mohammed da Bukola Saraki da su rike tutar PDP daga Arewa.
Daily Trust ce ta rahoto kungiyar nan ta NEF ta bakin darektanta na yada labarai da wayar da kan al’umma, Hakeem Baba-Ahmed, ya na karin haske a kan maganar.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa masu neman takara a PDP ne suka kawo maganar a fito da ‘dan takara guda daga Arewa a cikinsu ta hanyar yin maslaha.
Bala Mohammed, Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Mohammed Hayatudeen ne suka samu Ibrahim Badamasi Babangida su na neman ya fito da guda a cikinsu.
Kamar yadda Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana a jawabin da ya fitar, tsohon shugaban kasar ya bukaci Farfesa Ango Abdullahi ya tsara yadda za a iya samun mafita.
Aikin Ango Abdullahi ne
A matsayinsa na gashin kansa, Ango Abdullahi ya fito da ka’ida da tsarin yadda za a bi a tsaida wanda ake ganin zai wakilci Arewa wajen neman tikitin PDP a 2023.
Baba Ahmed ya ce tsohon shugaban jami’ar ta ABU Zaria ne ya yi wannan ba kungiyar NEF ba, ya ce babu inda dattawan Arewa a matsayin kungiya su ka shiga lamarin.
"Kungiyar NEF ba ta da alaka da wata jam’iyyar siyasa ko ‘dan takara, kuma da gaske ta ke yi wajen ganin an yi adalci wajen fito da shugabanni a zaben 2023.”
Daga Fara Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Ta Yi Wuff Da Wani Matashi a Najeriya, Hotunansu Ya Ɗauki Hankula
“Haka zalika ta nanata bukatar kowane yanki na kasar nan ya taka rawar gani. NEF ta na ganin ‘yan jam’iyya ne za a bari su tsaida wanda za su yi takara.”
- Dr. Hakeem Baba-Ahmed
Ra'ayin Paul Unongo ya saba
Jaridar ta rahoto jagoran kungiyar dattawa, Paul Unongo yana kare matsayar da aka dauka na fito da Bukola Saraki da Bala Mohammed a matsayin ‘yan takara a PDP.
Paul Unongo ya shaidawa manema labarai a garin Jos cewa shi ya fara kawo wannan shawara, kuma aka yi taro a Abuja, aka yarda a ba Arewa maso tsakiya tikiti.
Adamu Garba na neman kudin takara
Adamu Garba ya nuna da gaske yake yi wajen neman takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki, duk da ya yi mamakin jin yadda APC ta tsawwala kudin fam.
Malam Adamu Garba II bai da niyyar hakura da burin na sa domin an ji labari ya fito da lambar akawun da mutane za su rika aika masa da gudumuwa ta banki.
Asali: Legit.ng