Zaben 2023: APC Ta Ɗage Fara Sayar Da Fom Ɗin Takara, Ta Bayyana Dalili

Zaben 2023: APC Ta Ɗage Fara Sayar Da Fom Ɗin Takara, Ta Bayyana Dalili

  • Jam’iyyar APC ta dage siyar da fom din tsayawa takara na duka matakai a ranar Asabar har sai baba ta gani saboda wanda aka bai wa kwangilar yin fom din be yi akan lokaci ba
  • Dama ranar Laraba bayan kammala taron Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar ta kasa, NWC, Sakataren watsa labaran jam’iyyar, Felix Morka ya ce za a fara siyar da fom din ranar a Asabar
  • Sai dai har ranar Juma’a Shugabancin tsare-tsaren jam’iyyar APC ba ta ga ko fom daya ba, kuma akwai majiyar da ke nuna cewa jam’iyyar bata shirya komai ba na zaben fidda gwanin da za ta yi tsakanin Mayu da Yuni ba

Yanzu haka batun siyar da fom din takara na ko wanne mataki na jam’iyyar APC wanda za a fara yau (Asabar) ya tsaya cak sai baba ta gani, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

Wannan ya biyo bayan yadda dan kwangilar da aka sa yin fom din ya kasa yi a lokacin da aka yi alkawarin zai kammala kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

APC Ta Dage Fara Sayar Da Fom Ɗin Takara, Ta Bayyana Dalili
APC ta dage siyar da fom din takara har sai baba ta gani. Hoto: The Punch.
Asali: Facebook

Bayan kammala taron Kwamitin gudanarwar jam’iyyar a ranar Laraba, sakataren watsa labaran jam’iyyar APC, Felix Morka, ya shaida cewa jam’iyyar za ta a fara siyar da fom din takara a ranar Asabar.

A ranar Juma’a kuma Shugabancin APC din ba ta ga ko fom daya ba daga wurin dan kwangilar.

Ko a ranar Asabar, The Punch ta tattaro cewa jam’iyyar bata kammala shirye-shiryen fara siyar da fom din ba da kuma gudanar da zaben fidda gwaninta da ya kamata a yi tsakanin ranar 18 ga watan Mayu da 1 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

Ana sa ran zuwa karshen mako za a kammala fom din

Yayin tattaunawa da wakilin Punch, wata babbar majiya ta jam’iyyar wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta ce har yanzu ba a tsayar da ranar da za a fara siyar da fom din ba.

Kamar yadda majiyar ta shaida:

“An dage batun siyar da fom din da ya kamata a fara yi gobe (Asabar). Kawo yanzu ba a tsayar da ranar da za a fara siyarwa ba. Ranar Litinin NWC za ta sanar da ranar da aka mayar.
“An dage ranar ne bayan dan kwangilar da aka sa ya samar da fom din ya kasa yi akan lokaci. Yanzu haka (ranar Juma’a da yamma) a batun da muke yi ba a kawo fom din ba. Amma muna sa ran zuwa mako mai zuwa za a fara siyarwa saboda cikin ranakun karshen mako ake sa ran dan kwangilar zai kawo.”

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Jam'iyyar APC ta faɗi gaskiyar abinda ya sa ta sanya kuɗin Fom Miliyan N100m

Ana cikin wannan yanayin ne aka samu rahoton bayar da umarnin dakatar da darektocin jam’iyyar APC 6 na Gidan Buhari daga ranar Juma’a.

Wannan daya ne daga cikin matakan da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar ta dauka don gyara a babban ofishin jam’iyyar.

Cikin wadanda sabon umarnin ya shafa har da shugaban bangaren dokokin jam’iyyar.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164