N50m na ware tun farko, Minista ya fadi hanyar da zai tara N100m na sayen fam a APC
- Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa bai yi tunanin tsadar fam din shugaban kasa zai kai N100m ba
- Amma duk da haka Ministan ya hakikance a kan yin takara, har ya bayyana wasu manufofinsa
- Ngige ya na sa rai magoya bayan da yake da shi a Najeriya za su yi karo-karo domin ya mallaki fam
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta yanke kudin fam din shiga zaben takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 100 a zabe mai zuwa da za ayi a 2003.
Premium Times ta rahoto Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ya na cewa ya yi lissafin zai kashe Naira miliyan 50 ne wajen sayen fam.
Wannan lissafi ya ruguje da APC ta fito da farashin da aka tsaida a wajen taron majalisar NEC.
A wata hira da aka yi da shi, Sanata Chris Ngige ya shaidawa manema labarai cewa magoya baya za su taimaka su hada masu kudin da zai yanki fam din.
Da yake bayani a ranar Alhamis, Ministan ya fadawa Channels TV cewa ba zai soki jam’iyyarsa ta APC a kan yadda ta tsawwala kudin fam din shiga takaran ba.
Ngige ya kare APC NEC
“Ko na ji dadin abin da ya faru, ko ban ji ba, ba abin la’akari ba ne. Abin da majalisar NEC ta jam’iyya da tayi kenan, ba zan soke su ba." - Chris Ngige.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ngige ya yi kokarin kare jam’iyyarsa ta APC mai mulki, ya ce an lafta kudin fam ne saboda bayan zabe, ‘ya ‘yan jam’iyya ba su kawo mata wata gudumuwa.
“…Naira miliyan 50 na yi kasafi…ina da magoya baya, ka da ka damu da ni. Za su tara mani gudumuwa.” = Chris Ngige.
APC za ta kai labari a 2023?
An kuma rahoto tsohon gwamnan na Anambra yana cewa za a fafata a zaben fitar da gwanin, amma ya ce yana sa ran wanda ya fi cancanta zai yi nasara.
Sanata Ngige ya ce idan ya zama shugaban kasa, zai amincewa jihohi su kafa rundunar ‘yan sandansu, a ganinsa wannan zai kawo zaman lafiya a ko ina.
'Dan siyasar ya ce a cikin shekaru biyu, za a ga tasirin gwamnatinsa idan ya zama shugaban kasa. Ngige ya na mai sa ran APC za ta doke jam'iyyar PDP a 2023.
Amosun na shirin shiga takara
An samu labari cewa Sanata mai wakiltar mazabar Ogun ta tsakiya, Ibikunle Amosun yana daf da bada sanarwar cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a APC.
Idan an fara saida fam a ranar Asabar, an san cewa Ngige da su Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Yahaya Bello da Dave Umahi za su saye na su.
Asali: Legit.ng