APC, PDP, SDP: Farashin fom din takara a manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya
Gabanin zaben 2023, yawancin jam’iyyun siyasa sun kayyade farashin tsayawa takara da kudin fom dinsu, lamarin da ya girgiza 'yan Najeriya da dama.
A cikin wannan labarin, Legit.ng Hausa ta jero kudaden da ake kashewa wajen sayen fom din takara a kujeru daban-daban ga mai son tsayawa takara a Najeriya a zabe mai zuwa, kamar yadda TheCable ta tattaro.
Ga su kamar haka:
PDP
- Shugaban kasa - N40m
- Gwamna - N21m
- Majalisar Dattawa - N3.5m
- Majalisar Wakilai ta kasa - N2.5m
- Majalisar jiha - N600k
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
APC
- Shugaban kasa - N100m
- Gwamna - N50m
- Majalisar Dattawa - N20m
- Majalisar Wakilai ta kasa - N10m
- Majalisar jiha - N2m
SDP
Shugaban kasa - N35m
Gwamna - N16m
Majalisar Dattawa - N3m
Majalisar Wakilai ta kasa - N1.7m
Majalisar jiha - N500k
Abin lura: Farashin na iya sauyawa a kowane lokaci, don haka za mu sabunta wannan jeri yayin da muka samu karin bayani.
Kofar rashawa: 'Yan Najeriya sun kadu da jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m a APC
A wani labarin, a jiya ne jam'iyyar APC ta yi zamanta gabanin zaben fidda gwani na 'yan takara a shirin zaben 2023 mai zuwa.
A taron ne jam'iyyar ta bayyana cewa, N100m za ta sayar da fom din takarar shugaban kasa yayin da ta ce a cikin kudi N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.
Wannan lamari ya sanya 'yan Najeriya da dama cikin rudani, har ta jau ga da dama suka tofa albarkacin bakinsu game da wannar manufa ta jam'iyyar mai ci a yanzu.
Asali: Legit.ng