2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna

2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna

  • Gabannin zaben 2023, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Mannir Yakubu, ya sauka daga mukamin kwamishinan noma
  • Yakubu ya yi murabus daga kujerar ne domin ya shiga fafutukar neman takarar kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa
  • Wannan mataki da ya dauka ya biyo bayan umurnin da Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar na cewa duk masu neman takara su sauka daga mukamansu

Katsina - Mataimakin gwamnan jihar Katsina, QS Mannir Yakubu, ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan noma a yayin da yake shirye-shiryen kaddamar da aniyarsa ta son yin takarar kujerar gwamna a zaben 2023.

Labarin murabus din nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaransa, Ibrahim Musa Kallah, ya saki a daren ranar Talata, Vanguard ta rahoto.

2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna
2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna Hoto: PM News
Asali: UGC

A cewar sanarwar, wannan hukunci nasa ya yi daidai da sashi 84 (12) na dokar zaben 2022 kamar yadda aka gyara ta.

Kara karanta wannan

Zulum ya yi rabon buhuhunan hatsi, kudi da atamfa ga mutum 100,000 a cikin garin Maiduguri da Jere

Dokar ta bukaci duk masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati dake neman yin takara a zabe su yi murabus daga mukamansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin gwamnan a cikin jawabin ya yi godiya ga Allah da Gwamna Aminu Masari kan dama da ya bashi na ci gaba da bayar da gudunmawa wajen dawo da harkar noma a jihar karkashin mulkinsa.

Mannir ya kuma nuna jin dadinsa kan sake fasalin bangaren noma inda manoman suka samu sauyi wajen noma wanda ke tabbatar da tsaron abinci da bukatun noma a jihar da ma Najeriya baki daya, rahoton PM News.

Sanata mai wakiltan yankin Buhari ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a hukumance

A wani labarin, Ahmed Babba Kaita, sanata mai wakiltan yankin Katsina ta arewa, wato mazabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

Premium Times ta rahoto cewa Mista Babba-Kaita ya sanar da cewa ya koma jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) mai adawa, a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu.

Sauya shekar nasa ya kawo karshen rade-radin da ake ta yi a gidajen radiyo a Katsina da kuma shafukan soshiyal midiya cewa sanatan zai sauya jam’iyyar siyasa gabannin babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng