Kofar rashawa: 'Yan Najeriya sun kadu da jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m a APC

Kofar rashawa: 'Yan Najeriya sun kadu da jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m a APC

  • 'Yan Najeriya sun bayyana kaduwarsu da jin labarin za a sayr da fom din takarar shugaban kasa a kan kudi N100m
  • Wannan na zuwa dalilin sauya farashin sayen foma-foman takara a Najeriya na jam'iyya mai mulki; APC
  • 'Yan Najeriya sun yi imani da cewa, irin wannan tsadar ke kai ga cin hanci da rashawa a Najeriya

Najeriya - A yau ne jam'iyyar APC ta yi zamanta gabanin zaben fidda gwani na 'yan takara a shirin zaben 2023 mai zuwa.

A taron ne jam'iyyar ta bayyana cewa, N100m za ta sayar da fom din takarar shugaban kasa yayin da ta ce a cikin kudi N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.

Wannan lamari ya sanya 'yan Najeriya da dama cikin rudani, har ta jau ga da dama suka tofa albarkacin bakinsu game da wannar manufa ta jam'iyyar mai ci a yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: N100m zamu sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC

Martanin 'yan Najeriya kan kudin fom N100m
Martanin 'yan Najeriya bisa jin farashin fom din takarar shugaban kasa N100m | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ba a bar daya daga cikin matasa 'yan takarar shugabancin kasar nan a baya a wannan martani, inda ya bayyana kaduwarsa a shafin Twitter.

Legit.ng Hausa ta zuba ido kan maganganun da 'yan Najeriya ke yi, inda muka tattaro muku wasu daga ciki domin kusan halin da ake ciki.

Wasu 'yan Najeriya sun nuna rashin dacewar hakan

Ga kadan daga abin da suke fadi:

@Chypee3 ya ce:

"Kenan yanzu osibanjo na #100m na siyan tikiti amma ba su da kudin da za su sasanta ASUU domin mu fara makaranta."
"Omo!!! Ina tare da Peter Obi jaw"

@Adedeji__O ya ce:

"#100m na tikitin takarar shugaban kasa a APC.
"Wannan ne dalilin da yasa wadannan mutanen ke yin duk mai yiwuwa don cin zabe. Bayan cin zabe, inda hankalinsu zai karkata shine yadda za su mayar da uwar kudinsu. Kai! "

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

@noahson08 ya ce:

"Shugaban kasa #100m ..daya daga dalilin da ke sa wadannan mutane su wawure kudade kenan..."

@OlawaleyDc ya ce:

"#100m na takarar shugaban kasa, woow,
"Bari in hadiye burina kuma a haka kuna son matasan da ba sa cin hanci da rashawa ko wadanda ’yan siyasa suka lalata da cin hanci da rashawa su yi mulki."

Wasu kuma basu ga laifin APC ba

A bangare guda, wasu 'yan Najeriya sun nuna cewa, matasa za su iya sayen fom din takarar matukar suka hada kawunansu wuri guda.

Ga kadan daga abin da wasu ke cewa:

@BIGCKAY234 ya ce:

" Matasa ne suka tara gudunmawar sama da miliyan 100 ga Davido, tabbas za su iya ba wa dan takarar da suke so. Lokaci ya yi da matasa za su tsunduma cikin harkokin siyasa ba wai kawai su zauna su yi ta cece-kuce a cikin dakunansu ba."

@eagle_judyino

"Jam’iyyar Apc ta yi wa 'yan jam’iyyarta haka ne domin sun san mutanen da ke neman mukamai daban-daban, galibinsu mutane ne masu fada aji ko rike da wani mukami na siyasa, kuma suna da tarin kudi da yawa. Saboda haka, za su iya biya."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

N100m muke sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC

A wani labarin, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yanke shawara kan farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar kujerar shugaban kasa a 2023 karkashin lemarta.

APC ta ce naira milyan dari kowani dan takara zai biya don yankan Fom. A cikin kudi N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.

Wannan na cikin abubuwan da aka yanke shawara kansu a taron majalisar zartaswar jam'iyyar da aka yi ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.