Kusan 'yan takara a 2023: Jerin mutum 41 da ke hanyo gaje kujerar Buhari a zaben 2023
A yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke gabatowa, ‘yan siyasa da dama daga jam’iyyu daban-daban na bayyana ra’ayinsu na hawa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
An yi imanin cewa wasu mutane har yanzu suna saka yiwuwar ayyana aniyarsu, yayin da wasu wadanda ke ciki dumu-dumu, a halin yanzu ke neman goyon baya da shawarwari daga masu ruwa da tsaki da magoya baya.
A halin yanzu dai akwai akalla mutum 41 da ke son tsayawa takarar shugabancin kasar nan daga jam’iyyun siyasa kamarsu APC PDP, ADC, PRP, SDP, APGA, AP, da AAC.
Jerin sunayen ‘yan takara a jam’iyyun da aka ambata a sama sune kamar haka:
'Yan takara daga jam'iyyar APC
Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Mohammed Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
- Prof Yemi Osinbajo
- Chief Rotimi Amaechi
- Dr. Chris Ngige
- Governor Yahaya Bello
- Ibinabo Joy Dokubo
- Ihechukwu Dallas-Chima
- Senator Orji Uzor Kalu
- Engr Dave Umahi
- Rev Moses Ayom
- Senator Rochas Okorocha
- Gbenga Olawepo-Hashim
- Ibrahim Bello Dauda
- Dr. Tunde Bakare
- Tein Jack-Rich
Daga jam'iyyar PDP
- Senator Bukola Saraki
- Senator Anyim Pius Anyim
- Peter Obi
- Alhaji Atiku Abubakar
- Dr Nwachukwu Anakwenze
- Sam Ohuabunwa
- Olivia Diana Teriela
- Dele Momodu
- Ayo Fayose
- Muhammed Hayatu-Deen
- Senator Bala Mohammed
- Alhaji Aminu Tambuwal
- Udom Emmanuel
- Nyesom Wike
- Chief Charlie Ugwu
Daga jam'iyyar ADC
- Prof Kingsley Moghalu
- Chukwuka Monye
- Dr. Mani Ibrahim
- SDP
- Adewole Adebajo
- Khadijah Okunnu-Lamidi
- PRP
- Patience Key
- Chief Kola Abiola
Jam'iyyar APGA
- Angela Johnson
Jam'iyyar AP
- Professor Christopher Imunolen
Jam'iyyar AAC
- Omoyele Sowore
Madam Nonye Josephine Ezeanyaeche
2023: Hadimin Shugaban Kasa ya koma gida, zai shiga takarar ‘Dan Majalisa a Kano
A wani labarin, mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a kafofin sada zumunta na zamani, Bashir Ahmaad ya na shirin takarar ‘dan majalisa a zaben 2023.
Malam Bashir Ahmaad ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a ranar Talata. Ahmaad zai nemi kujerar Gaya/Ajingi/Albasu a majalisar wakilan tarayya.
Da yake bayani a shafin na sa, hadimin shugaban kasar ya tabbatar da cewa ya ziyarci mahaifarsa watau Gaya da ke wajen birnin Kano a cikin makon nan.
Asali: Legit.ng