Marafa ya ragargaji APC, amma ya karyata rade-radin sauya-sheka zuwa Jam’iyyar PDP
- Kabiru Marafa ya fito ya shaidawa Duniya cewa zuwa yanzu bai shiga jam’iyyar adawa ta PDP ba
- Tsohon Sanatan na jihar Zamfara ya ce labarin da yake yawo na sauya-shekarsa ba gaskiya ba ne
- Marafa ya ce dole su bar APC domin an zalunce su, kuma har su na tattaunawa da wasu jam’iyyu
Zamfara - A karshen makon da ya wuce ne aka ji Sanata Kabiru Marafa ya yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki, ya shiga PDP., hakan ba ta tabbata ba.
A wata hira da ya yi da jaridar Tambari Hausa TV, Kabiru Marafa ya karyata wannan labari, ya ce kawo yanzu bai sauya-sheka daga jam’iyyar APC ba.
A wannan tattaunawa da aka yi da shi, tsohon Sanatan na jihar Zamfara ya kira abin da tsofaffin shugabannin APC suka yi masu da ‘rashin hankali’.
“Ban san labarin na ka ba, da kuma yadda ka ji shi. Amma abin da na sani shi ne akwai jam’iyyu (ba PDP kadai ba) da la’akari da rashin hankalin da tsofaffin shugabannin APC suka yi mana (mu mutanen Zamfara), sun neme mu.”
“…Da mu zo su yi mana abin da jam’iyyarmu ta APC ba ta iya mana ba. Ma’ana, su yi mana adalcin da jam’iyyarmu (APC) ta gaza yi mana.”
“Kuma mu na tattaunawa da su har yanzu, a iyaka sani na, ba mu kai karshe da kowace jam’iyya ba har yanzu cewa za mu bi ta, ko ba za mu bi ta ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Kabiru Marafa
"Kuskure ne aka yi"
Babban ‘dan siyasar ya yi mamakin jin labarin sanarwar komawarsu PDP, inda ya tabbatar da cewa kuskure ne aka yi, kuma ya yi kira ayi watsi da batun.
Kabiru Marafa wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 ya ce shakka babu, jam’iyyu da-dama su na zawarcin tsagin su.
Daga cikin jam’iyyun hamayyan da suka nemi tsagin su Marafa su shigo tafiyarsu akwai PDP, NNPP, Accord Party kamar yadda ya shaida da bakinsa a jiya.
Maganganun barin APC
“Wannan gaskiya ne, idan ka yi la’akari da zaluncin da wancan tsohon shugabancin da APC ya yi mana, mu na da wani zabi da ya wuce haka nan? Ai babu!”
- Kabiru Marafa
Har ila yau, Sanata Marafa ya bayyana cewa sabon shugaban APC, Abdullahi Adamu ya nemi ya zauna da jagoran na sa, Abdulaziz Yari a kan rikicin Zamfara.
Marafa ya ce tsohon gwamna Yari zai yi tafiya don haka ya bada sunansa ya wakilce shi wajen zama da sabon shugaban jam’iyyar na kasa da nufin a sasanta.
Labarin da yake yawo
Rahoton da mu ka kawo a ranar Lahadi shi ne, kam'iyyar APC ta rasa manyan jiga-jiganta biyu a jihar Zamfara, tsohon gwamna Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa
Wannan labari ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban PDP na jihar Zamfara, Kanal Bala Mande mai ritaya ya fitar ga manema labarai a garin Gusau.
Asali: Legit.ng