Bai dace kuna Instagram ba amma baku da katin zabe, Tinubu ga matasa
- Bola Tinubu ya ce bai kamata matasa su cigaba da kokawa ba, kamata ya yi su hada kai wajen ganin Najeriya ta zama daya
- A cewarsa, bai dace a ce matasa suna ziyartar kafafan sada zumuntar zamanin ba, bayan basa da katin zaben da zasuyi zabe ba
- Ya fadi hakan ne a taron matasan APC na kudu maso yamma, inda ya bukaci su mara masa baya wajen ganin an canza labarin da kasar ke ciki daga bisani a mika ta garesu
Legas - Bola Tinubu, dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC mai fatan gaje kujerar shugaba Buhari, ya ce bai kamata matasa su cigaba da kokawa ba, The Cable ta ruwaito.
Tsohon gwamnan Legas din ya shawarci matasa da su yi aiki tukuru wajen ganin sun gina sabuwar kasar da zata samar da dama da cigaba mara iyaka.
Tinubu ya ce bai kamata matasa su cigaba da ziyartar kafafan sada zumuntar zamani irinsu Instagram ba, bayan basa da katikan zaben da zasu zabi shugabannin da suke so.
Yayi jawabin ne a ranar Asabar a zagayen da matasan kudu maso yamman jam'iyya mai mulki suka yi.
Zagayen ya gabata ne a filin wasannin Mobolaji Johnson cikin Onikan dake Legas, inda matasa karkashin jagorancin Matasan kudu maso yamma masu tasowa.
A ruwayar Channels TV, tsohon gwamnan Legas din ya ce:
"Na iso nan, ba don kaina ba, sai don ku da daukacin matasan da zasu wakilcemu a gaba. Muna bakin ciki idan kun shiga bakin ciki; ba zan taba ganin laifinku don wannan ba. Alkawuran baya basu isa su taimake ku don gina rayuwarku ta gaba ba tun farko.
"Amma, ban yarda da uzirurruka na cewa ba zamu iya taimakawa ba; zamu iya taimakawa. Abunda kuke bukata shi ne karfin guiwa, jajircewa da tabbata a kan kudurinku. Dole sai kun sa a ranku zaku iya; dole sai kuna da kokari da jajircewa don canza labarin talauci da ta'addanci."
Ya kara da cewa:
"Ba zamu cigaba da kokawa a kan abunda ya wuce ba. Dole mu mu daura janjami don samar da sabuwar Najeriya. Dole ku shiryawa aikin dake gabanku. Idan kun san baku da katin zabe kuje ku yi. Idan kuma kuna dashi, ku je ku sake sabunta katin naku.
"Bai kamata ku zama daga cikin 1.4 biliyan na matasan da ke amfani da Instagram, bayan baku da PVC da zaku yi zabe ba. Matasa su ne dalilin da yasa na tsaya takara. Ina so in zama shugaban ku baki daya; ku yi kokari don kaini wannan matakin."
Dan takarar shugabancin kasan ya cigaba da cewa:
"Abunda ya dace mu yi shi ne mu gina Najeriya guda daya. A lokacin da muka fara a Legas, mu kan dauke gawawwaki a kan titina. Gashi a yau, Legas na daya daga cikin jihohin da suka fi saura samun cigaba.
"Zamu iya gina Najeriya, inda jin dadi ba zai kebanta ko ya yi karanci ga iyalan talakawa ba. Najeriya guda daya ita ce mafarkinmu, Najeriya mai yanci ita ce kokarinmu, sannan Najeriya ta kubuta daga rikici shi ne abunda muka yi alkawarin zamu mika ta gareku."
Matasa sun yi alkawarin goyawa Tinubu baya, wanda suka siffanta da "Dan takara mai hangen nesa da sanin sirrin rike kasa".
Yayin martani, Tinubu ya siffanta zagayen magoya bayan nashi da "babbar nasara", inda ya ce zai nuna godiya ga yadda suka mara masa baya don aiki tukuru don ganin an canza labarin kasar ga matasa.
Asali: Legit.ng