2023: Zan Cigaba Daga Inda Jonathan Ya Tsaya, In Ji Ɗan Takarar Shugaban Kasa A PDP
- Tsohon sakataren Gwamnatin Tarayya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Anyim Pius Anyim, ya fadi kudirinsa idan ya hau mulki
- Yayin tattaunawa da Kwamitin Ayyukan jam’iyyar PDP, ya ce yana so ne ya dasa daga inda Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya a 2015
- A cewarsa, zai iya kawo karshen matsalolin da suka addabi Najeriya kasancewar ya dauki lokaci mai tsawo na rayuwarsa wurin hidima a fadar shugaban kasa
Anyim Pius Anyim, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya ce yana so a ba shi dama don ya ci gaba daga inda tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Anyim lokacin da ya tattauna da Kwamitin Ayyukan jam’iyyar PDP, yana so ya ci gaba da ayyukan da aka baro tun 2015 amma dole sai an yi amfani da dabaru masu yawa wurin bubbugo da tattalin arzikin Najeriya sannan a mayar da kasar cikin zaman lafiya da ci gaba.
Ya kwatanta kansa a matsayin mutumin da ke kawo karshen rigima kuma wanda ya ke da duk dabaru, dabi’u da halayen da zai kawo mafita ga matsalolin kasar nan.
‘Yan Najeriya suna cikin damuwa akan halin da kasa take in ji Anyim
Anyim ya ce ‘yan Najeriya suna cikin damuwa akan halin da kasar take ciki kuma suna bukatar gwamnati ta mayar da ita yadda ta sameta a 2015, don haka ba su da hujjar rashin zabensa.
Ya kara da cewa:
“Yayin da na yi aiki a majalisar dattawa, na ga matsalolin da dama kuma da kawo musu mafita. Idan ka yi tunani, tattalin arzikinmu duk ya rushe.
“A halin da muke ciki, akwai dabarun da zamu yi wurin bai wa kasashen waje kwarin gwiwar siyan kaya a wurinmu, amma ba a dare daya ake yi ba. Idan ku ka goya min baya, zan dawo da kasar nan turbar zaman lafiya, ci gaba da daukaka.”
Buhari Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Yana Ta Cika Wa 'Yan Najeriya Alƙawuran Da Ya Ɗauka Yayin Kamfen Ɗin Zaɓen 2015
Ya hori ‘yan PDP akan su kiyaye maimaita kuskuren da suka tafka a 2015
National mail Online ta ruwaito inda ya ci gaba da cewa:
“Kuskuren da ya kamata mu kiyaye shi ne wanda muka yi a 2015. A 2015 wasu daga cikinmu sun kware wa jam’iyyarmu baya inda suka koma lalube a duhu, shiyasa yanzu muke fama. Kasar nan tana bukatar tallafin mu.”
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyan ya ce kasar nan tana bukatar wanda zai daidaita ta, kuma shi ne kwararre a wannan fannin.
Ya ci gaba da cewa a duk shekarun da ya yi yana aiki, hidima ya dinga yi wa Gwamnatin Tarayya. Ya yi aiki da wata ma’aikata karkashin Gwamnatin Tarayya, ya rike matsayin shugaban majalisar dattawa sannan ya rike kujerar Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda nan ne asalin cibiyar aikin fadar shugaban kasa.
Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan
A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.
Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.
Asali: Legit.ng