Babbar Matsala ta kunno kai a APC, Wani Babban jigo ya fice daga jam'iyyar, ya koma PDP

Babbar Matsala ta kunno kai a APC, Wani Babban jigo ya fice daga jam'iyyar, ya koma PDP

  • Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a jihar Oyo, Mogaji Joseph Tegbe, ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP
  • Rahoto ya nuna cewa Tegbe ya ɗauki wannan matakin tare da canza mazauni domin tsayawa takarar Sanatan Oyo ta tsakiya
  • Wani Jigon APC a jihar ya bayyana cewa matakin ficewar Tegbe bai musu daɗi ba, amma ba'a masa adalci a jam'iyya

Oyo - Siyasar jihar Oyo ta ɗauki wani sabon salo yayin da ɗaya daga cikin yan takarar kujerar gwamna karkashin APC dake jan zaren sa a jihar, Mogaji Joseph Tegbe, ya koma PDP.

Wannan cigaban na zuwa ne a dai-dai lokacin da rikici ya samu gindin zama a cikin jam'iyyar kawo cigaban, wanda ya yi sanadin rasa jigonta, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Tsohon mamban APC ya tabbatar da komawarsa PDP ne ranar Talata da daddare bayan jure matsin lamba ta kowane ɓangare na tsawon watanni.

Kara karanta wannan

Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

Dan takara ya koma PDP daga APC.
Babbar Matsala ta kunno kai a APC, Wani Babban jigo ya fice daga jam'iyyar, ya koma PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sabon ɗan jam'iyyar PDP ya shirya canza wuri daga kudu maso gabashin Ibadan a jihar Oyo, zuwa ƙauyensu dake ƙaramar hukumar Ona-Ara a mazaɓar Sanatan Oyo ta tsakiya.

Mista Tegbe, wanda ya yi karatun Injiya a jami'ar Obafemi Awolowo, ya shahara ne bayan ya yi yaƙin neman zaɓe na tsawon watanni hudu a 2018, har zuwa sanda APC ta ba Bayo Adelabu tutar takarar gwamna.

Meyasa ya zaɓi barin APC a yanzu?

Bayanai sun nuna cewa PDP ta masa alƙawarin tikitin takarar Sanatan Oyo ta tsakiya, ya ture tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin gwamna Makinde, Bisi Ilaka.

Wata majiya mai ƙarfi ta ce tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Monsurat Sunmonu, shi ya yi ruwa ya yi tsaki har aka cimma matsaya.

Wani babban jigo a tsohuwar jam'iyyar Tegbe ya ce:

Kara karanta wannan

Osinbajo ya fita da APC ta Legas, ya koma ta jihar Ogun: Mai magana da yawunsa

"APC ta wulaƙanta shi, duk da ban ji daɗin matakin da ya ɗauka ba, amma Injiniya Tegbe yana da mabiya da yawa, tabbas lamarin zai shafi jam'iyyar mu."

A wani labarin kuma Wani Gwamnan APC ya gana da Buhari, ya faɗa masa aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, ya gana da Buhari kan niyyarsa ta neman shugaban ƙasa a 2023.

Gwamnan ya sanar da shugaban ƙasa aniyarsa kuma Buhari ya ƙara masa kwarin guiwa da sanya masa albarka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel