2023: Jigon APC Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Irin Ƴan Siyasan Da Ya Kamata Su Ƙaurace Wa

2023: Jigon APC Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Irin Ƴan Siyasan Da Ya Kamata Su Ƙaurace Wa

  • Wani jagoran APC, Gbenga Olawepo-Hashim, ya ja kunnen ‘yan Najeriya akan zaben wadanda ke gwamnati tun 1999 a zaben shugaban kasa na shekarar 2023
  • A cewarsa, ‘yan Najeriya ba za su samu canjin rayuwa da kasa ba kamar yadda suke buri idan har suka zabi dan siyasar da ke gwamnati tun shekaru 23 da suka gabata
  • Olawepo-Hashim ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2019, kuma ya bayar da wannan shawarar yayin tattaunawa da manema labarai ranar Laraba

Wani jigo na jam’iyyar APC, Gbenga Olawepo-Hashim ya shawarci ‘yan Najeriya akan zabinsu na shugaban kasa a shekarar 2023, inda ya ce su kiyayi zaben dan siyasar da ya ke gwamnati tun shekarar 1999, The Punch ta ruwaito.

Kamar yadda ya ce, kada ‘yan Najeriya su sa ran samun wani ci gaba da sauyi mai kyau a kasar nan idan har suka zabi dan siyasar da ke gwamnati tun shekaru 23 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Jigon APC Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Irin Ƴan Siyasan Da Ya Kamata Su Ƙaurace Wa
Kada ku zabi yan siyasar da suke mulki tun 1999, Jigon APC ya shawarci yan Najeriya. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Olawepo-Hashim ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar People’s Trust a zaben 2019, kuma ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Laraba yayin tattaunawa da manema labarai.

Ya ce wanda ya kwashe shekaru 23 a gwamnati ba zai san hanyoyin sauya Najeriya ba

Information Nigeria ta ruwaito yadda ya ce:

“Maganar gaskiya akwai wadanda suka dade a gwamnati kuma sun saba da rashawa, don haka yaudarar kai mutum zai yi idan har ya zabe su don su yi yaki da rashawa.”

Yayin bayani akan cewa wanda ya saba da rashawa ba zai iya yakar rashawa ba, ya ce kasar nan tana bukatar a kakkabe munanan abubuwan da suka same ta a baya, matsawar ana so a ci gaba.

Olawepo-Hashim ya kara da cewa:

“Ko dai a APC ko PDP ko kuma wata jam’iyyar ta daban, wadanda suka dade a gwamnati ba su yi wani abin kirki ba face satar kudin gwamnati, yawo da ayarin motocin da ba sa sanya musu mai da kansu, kasa gyara kasa da sauran barnace-barnace.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

“Ina yin dariya idan na ji wanda bai taba zama a shagon mai aski ba a rayuwarsa yana yi wa matasa alkawarin samar musu da ayyukan yi. Wadannan mutanen ba su san yadda ake yin sana’o’i ba.
“Hanyar kawo karshen rashin tsaron kasar nan, matsalar rashin aiki, tsadar man fetur da sauran kayan masarufi suna bukatar a tunkare su ta sabuwar hanyar. Wadanda suka yi shekaru 23 a mulki ba za su gane ba.”

Ya bayyana kudirinsa idan ya hau mulki

Ya ce abinda ya ja hankalinsa akan APC shi ne yadda shugaban kasa ya yi amanna da cewa sai an kawo karshen rashawa, kuma rashawa ce ke kawo koma-baya a ci gaban kasar nan.

Olawepo-Hashim wanda ake sa ran zai sanar da ‘yan Najeriya kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa kafin karshen watan nan ya yi alkawarin bayyana wa ‘yan Najeriya burikansa akan muhimman abubuwa kamar tsaro, ayyukan yi, samar da isasshen man fetur, wutar lantarki, kawo karshen rashawa, kawo ci gaba a fannin lafiya, ilimi, masana’antu da sauransu.

Kara karanta wannan

Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164