Zaben 2023: Jerin sunayen masu takarar shugaban kasa na APC da PDP

Zaben 2023: Jerin sunayen masu takarar shugaban kasa na APC da PDP

Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, akwai yiwuwar manyan jam’iyyun siyasar kasar na All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) su gabatar da yan takararsu na shugaban kasa daga yanki guda.

A zahirin gaskiya, yan siyasa daga yankin arewa basa maraba da tsarin karba-karba a wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa.

A yanzu haka, wasu mutane sun dage cewa yan siyasa da dama daga arewa na iya shiga tseren neman shugabancin kasar domin wahalar da takwarorinsu na kudu.

Zaben 2023: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa na APC da PDP
Zaben 2023: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa na APC da PDP Hoto: APC
Asali: Twitter

A wannan rahoton, Legit Hausa ta lissafo jerin sunayen yan siyasa da suka nuna ra’ayinsu wajen neman kujerar daga manyan jam’iyyun siyasa biyu.

Wadanda suka ayyana kudirinsu a jam’iyyar APC sune:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Babban magana: Dubban 'yan APC da PDP a Katsina sun koma jam'iyyar su Kwankwaso NNPP

1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

2. Babban jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

3. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

4. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi

5. Tsohon gwamnan Abia kuma sanata mai ci, Orji Kalu

6. Tsohon gwamnan Imo kuma Sanata mai ci, Rochas Okorocha

7. Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya ce zai bayyana aniyarsa bayan watan Ramadan

Masu neman takarar shugaban kasa daga PDP wadanda suka siya tikitin takarar jam’iyyar na naira miliyan 40 sune:

1. Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar 2. Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

3. Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed

4. Gwamnan jihar Sakoto, Aminu Waziri Tambuwal

5. Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike

6. Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose

7. Tsohon manajan darakta na bankin FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen

Kara karanta wannan

2023: ‘Dan takarar APC ya musanya rade-radin hakura da neman zama Shugaban kasa

8. Mawallafin mujallar Ovation, Cif Dele Momodu.

2023: Idan Jonathan yace zai yi takara zan janye, Kauran Bauchi

A wani labarin, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan bai gama yanke shawarar ko zai yi takarar shugabancin kasar ba a 2023.

Mohammed ya bayyana hakan ne a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, yayin ganawarsa da kungiyar tsoffin ministocin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), rahoton Nigerian Tribune.

Ya bayyana cewa da ace tsohon shugaban kasar zai yi takarar kujerar a zaben 2023, toh da ba zai taba shiga tseren ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng