Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse

Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse

  • Sarkin Dutse, Mai martaba Nuhu Mohammadu Sanusi ya lamuncewa ministan sufuri, Rotimi Amaechi domin ya gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Basaraken ya bayyana matsayinsa ne a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, lokacin da ya karbi bakuncin Amaechi a fadarsa da ke garin Dutse, babbar birnin jihar Jigawa
  • Ya kuma jinjinawa tsohon gwamnan na jihar Ribas, cewa yana da duk cancantar da ake bukata daga wajen shugaba kuma shi mutum ne mai gaskiya

Jigawa - Mai martaba sarkin Dutse, Nuhu Mohammadu Sanusi, ya goyi bayan takarar ministan sufuri, Rotimi Amaechi, gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.

Da yake magana a yayin da ya karbi bakuncin Amaechi a fadarsa da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, Sanusi ya bayyana Amaechi a matsayin mutum mai gaskiya.

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Sarkin ya ce Amaechi na da dukkanin abun da kasar ke bukata daga shugaba, jaridar The Cable ta rahoto.

Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse
Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya ce:

“Shi mutum ne mai gaskiya, kuma kome za ka fada game da shi, ba za ka taba sauya gaskiyar cewa shi mutum ne mai gaskiya ba. Mutum ne mai karfin gwiwa. A duk inda ka gan sa za ka san cewa shine abun da ake kira da cikakken karfin gwiwa.
“Wadannan sune abun da ake so daga shugaba. Wadannan sune abubuwan da muke bukata a jagora musamman a yau, mutane masu kwarin gwiwa, wadanda za su iya fuskantar gaskiya da kalubale. Yana da juriya. Juriyarsa zan sake fada maku cewa, idan Amaechi na son cimma wani abu, ta kowani hali, zai nemi hanyar ganin ya same shi, saboda shi mai sadarwa ne.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

“Wannan ne dalilin da yasa na mara masa baya. Ina mutunta shi sosai kuma ina da karfin gwiwa a kansa. Ya cancanta sosai, kasancewarsa kakakin majalisa sau biyu. Shi ya fi cancanta.”

Amaechi ya mutunta Musulmai a lokacin da yake matsayin gwamnan Ribas

Basaraken ya ce Amaechi ya samawa Musulmai da Kirista wuri a Ribas a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar, rahoton Vanguard.

"A Najeriya, al'amura na kabilanci, siyasa da sauran su kan dauke mana hankali a kodayaushe amma anan ga wani dan Najeriya da na sani, kuma Amaechi dan Najeriya ne na gaskiya wanda bashi da kabilanci.
"Ya samawa Musulmai wajen ibadah a jihar Ribas wanda na fahimci cewa an lalata su bayan ya tafi, ya jure duk wulakanci da aka yi don ganin Musulmai sun muzanta a Porth Harcourt, kuma na san Allah zai saka masa da alkhairi.
"Na tabbata zai yi fiye da haka idan ya zama shugaban kasa. Da duk albarkatun da ke kasa, zai yi amfani da su wajen yaki da ta’addanci da sauran matsalolin da suka addabe mu, musamman a yankin arewa. Shi shingen alkhairi ne kuma mutum mai yawan haduwa da mutane.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

“Kimanin shekaru 16 da suka shige, wannan majalisa ta yanke shawarar daukar yara daga jihar Ribas, musamman daga karamar hukumarsa, Ikwerre, mun dauki yara 16, muka sanya su a makaranta tare da yarana, yawancinsu sun kammala karatu, wasun su sun yi aure a yanzu, kuma da na fada masa, ya yi godiya sosai kuma ina ganin mutuncinsa sosai sannan ina da kwarin gwiwa kan cancantarsa.”

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

A baya mun ji cewa Rotimi Amaechi, ministan sufuri na Najeriya, ya ce yana da kwarewar da ake bukata na zama shugaban Najeriya a zaben 2023.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ziyara, a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu, inji rahoton The Cable.

Amaechi ya bayyana cewa shi kadai ne dan takarar shugaban kasa da ya taba mulkar jihar da ake fama da rikicin ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng