2023: Gwamnan APC da Sanata zasu ayyana takarar shugaban ƙasa, sun sanar da Buhari

2023: Gwamnan APC da Sanata zasu ayyana takarar shugaban ƙasa, sun sanar da Buhari

  • Jiga-Jigan siyasa musamman masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun shirya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Sanata Ibikunle Amosun na shirin sanar da shirinsu na neman kujera lamba ɗaya
  • Cigaban na zuwa ne awanni 24 bayan mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya ayyana shiga takara a 2023

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti a kowane lokaci nan gaba zai iya sanar da aniyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Haka nan kuma wani ƙusan APC da ake tsammanin zai shiga tseren shine tsohon gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun, wanda ke wakiltar Ogun ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Daily Independent ta rahoto.

Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa manema labarai cewa mutanen biyu sun riga da sun sanar da shugaba Buhari burin dake zauciyarsu kuma ya sanya musu albarka.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mataimakin shugaban ƙasa zai yi buɗe bakin Azumi da Sanatocin Jam'iyyar APC

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
2023: Gwamnan APC da Sanata zasu ayyana takarar shugaban ƙasa, sun sanar da Buhari Hoto: Kayode Fayemi
Asali: Facebook

Gwamna Fayemi dai shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) kuma bayanai sun nuna cewa yana shirin cin gajiyar muƙaminsa.

A ɗaya bangaren kuma Amosun na ganin zai amfani da kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsa da shugaba Buhari, wacce ta samo asali tun lokacin da suke tare a jam'iyyar ANPP.

Waɗan da ke cikin tseren gaje Buhari a APC

Idan duk mutum biyu suka tabbatar da aniyarsu a hukumance, za su shiga jerin yan takara da suka haɗa da VP Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da takwaransa na Kogi, Yahaya Bello.

Sauran sun haɗa da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan Abia, Sanata Orji Kalu.

sai kuma gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin EmeFiele da ake yaɗa jita-jitar yana hangen shugabancin ƙasa karƙashin inuwar APC, amma har yanzun bai ayyana ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani da Hotuna: Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC jim kaɗan bayan Osinbajo ya shiga takarar 2023

Duk da har yanzun APC ba ta yanke yankin da zata kai takara ba, amma alamu sun nuna cewa zata ba ɗan kudu tutar takarar shugaban ƙasa, wanda ya haɗa da Kudu-Kudu, Kudu-Gabas da Kudu-Yamma.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ɗan yankin arewacin Najeriya ne.

A wani labarin kuma Bola Tinubu ya maida martani kan ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa

Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, da ɗansa bane.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnonin APC, Tinubu yace ɗan sa be girma haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262