Takara a 2023: Tinubu, Osinbajo da sauran jiga-jigan APC da suka ayyana nufin gaje shugaba Buhari

Takara a 2023: Tinubu, Osinbajo da sauran jiga-jigan APC da suka ayyana nufin gaje shugaba Buhari

  • A ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022, mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya shiga tseren gaje Buhari a hukumance
  • Kafin samun tutar takara karkashin APC, Osinbajo zai fafata da Tinubu, Amaechi da wasu mutum 4 da suka ayyana shiga takara
  • Mun tattaro muku baki ɗaya kusoshin jam'iyya mai mulki guda 7 da suka tabbatar da aniyarsu ga yan Najeriya

Abuja - Zuwa yanzun akalla mutum Bakwai suka ayyana aniyarsu ta neman takarar shugaban ƙasa a 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Sai dai akwai wasu yan takara da ake raɗe-raɗin suna da nufin neman kujerar amma har yau ba su bayyana wa duniya shirinsu ba, kamar gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

Cikakken Bidiyo: Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023

Yan takarar APC zuwa yanzu.
Takara a 2023: Tinubu, Osinbajo da sauran jiga-jigan APC da suka ayyana nufin gaje shugaba Buhari Hoto: guardian.com
Asali: UGC

Waɗan nan yan takarar ne ake zaton zasu gwabza a zaɓen fidda gwani domin samun tikitin takara na jam'iyya mai mulki.

A binciken da Legit.ng Hausa ta gudanar ya nuna cewa baki ɗaya yan takarar sun fito ne daga yankin kudu in banda gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Duk da har yanzun APC ba ta yanke yankin da zata ba takara ba, amma raɗe-raɗi ya yawaita cewa zata zaƙulo ɗan kudu ne ta bashi tutar takara.

Jerin yan takarar da suka faɗa wa Duniya nufin su a hukumance

1. Bola Ahmed Tinubu

2. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

3. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi

4. Tsohom gwamnan Abia kuma Sanata mai ci, Sanata Orji Kalu

5. Tsohon gwamnan Imo kuma Sanata mai ci, Sanata Rochas Okrocha.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Na maida mutum 2,000 sun zama Attajirai a jihata, Gwamnan Arewa dake son gaje Buhari

6. Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi

7. Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo

Ɗaga cikin duka waɗan nan yan yakara, Bola Tinubu, na cigaba da kai ziyara sassan kusoshin jam'iyya da ya haɗa da majalisar tarayya, yana baran goyon bayan su.

Haka nan, ya ziyarci shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, domin sanar da shi burinsa na ya gaje shi a babban zaɓen 2023.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta ba APC mamaki, ta lashe kujerun Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a Adamawa

Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta cigaba da jan zarenta a zaɓen kananan hukumomi.

Jam'iyya mai mulki ta lallasa abokiyar hamayyarta APC, ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi 21 da kuma Kansiloli 226.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262