Bayan ya koma PDP, Labaran Maku ya ayyana aniyarsa ta takarar kujerar gwamnan Nasarawa

Bayan ya koma PDP, Labaran Maku ya ayyana aniyarsa ta takarar kujerar gwamnan Nasarawa

  • Labaran Maku ya bayyana kudirinsa na son yin takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a zaben 2023 mai zuwa karkashin inuwar jam'iyyar PDP
  • A wannan karon, Makun ya dauki alkawarin yarda da sakamakon zaben fidda gwanin dan takarar jam'iyyar adawar a duk yadda ya zo
  • Ya bayyana hakan ne a garin Lafia, babbar birnin jihar a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, yayin da ya ziyarci uwar jam'iyyar a jihar

Nasarawa - Tsohon ministan labarai, Labaran Maku, ya ayyana aniyarsa ta son yin takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a babban zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Mista Maku wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya bayyana kudirinsa ne a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, a garin Lafia, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son gaje Buhari a 2023

Bayan ya koma PDP, Labaran Maku ya ayyana aniyarsa ta takarar kujerar gwamnan Nasarawa
Bayan ya koma PDP, Labaran Maku ya ayyana aniyarsa ta takarar kujerar gwamnan Nasarawa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne, lokacin da ya jagoranci magoya bayansa don sanar da kwamitin aiki na PDP a jihar game da batun dawowarsa babbar jam’iyyar adawar kasar.

Makun wanda kafin sauya shekar tasa ya kasance babban sakataren jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, na kasa ya baiwa mambobin PDP hakuri kan barin jam’iyyar da ya yi tun a 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa shi jajirtaccen dan jam’iyya ne kuma ya yi aiki a matakai daban-daban na jihar da tarayya kafin ya bar jam’iyyar saboda rashin gamsuwa da sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar a 2015.

Tsohon ministan ya ce koda dai ba zai iya gaskata dalilinsa na barin jam’iyyar ba, yana mai neman yafiyar mambobin jam’iyyar, inda ya kara da cewa ya yafewa dukkanin wadanda suka ci amanarsa a baya.

Dan siyasar ya ce zai yi takarar gwamna sannan ya dauki alkawarin karbar sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar, inda ya ce zai yi aiki tare da duk wanda ya samu tikitin domin kawowa jam’iyyar jihar a 2023. rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaba a Majalisar Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Shiga Wata Jam'iyyar

Ya ce jihar ta sha fama da matsalar rashin shugabanci nagari, rashin kokari daga jami’an gwamnati da kuma watsi da mutanen jihar a tsawon shekaru 12 da suka gabata.

Shugaban kasa: Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son gaje Buhari a 2023

A wani labarin kuma, babban faston Najeriya kuma limamin cocin Citadel Global Community Church, Tunde Bakare, ya ayyana aniyarsa ta son takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

A wani jawabi da ya yi a wani taron yanar gizo a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, Bakare ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta don jagorantar kasar daga shekarar 2023, Channels tv ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel