Dokubo Asari ya caccaki 'Dan takarar PDP, ya ce takararsa a 2023 ba za ta kai labari ba

Dokubo Asari ya caccaki 'Dan takarar PDP, ya ce takararsa a 2023 ba za ta kai labari ba

  • Alhaji Mujaheed Dokubo-Asari bai ganin cewa Gwamna Nyesom Wike ya dace ya rike Najeriya
  • A ra’ayinsa, Gwamnan na Ribas ba zai iya cin zabe ba, sannan bai yi kama da shugaban kasa ba
  • Mujaheed Dokubo-Asari ya taba jagorantar kungiyar tsagerun Niger Delta Peoples Volunteer Force

Rivers - Shugaban tsohuwar kungiyar tsagerun nan na Niger Delta Peoples Volunteer Force, Mujaheed Dokubo-Asari ya yi magana a kan zaben 2023.

Dokubo-Asari ya bayyana haka ne da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Arise TV a makon nan,

Alhaji Mujaheed Dokubo-Asari ya nuna cewa matakin da Gwamna Nyesom Ezenwo Wike ya dauka na yin takarar shugaban kasa, ba mai bullewa ba ne.

An rahoto tubabben tsageran wanda ya jagoranci kungiyar NDPVF, ya na mai cewa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike bai yi kama da shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu

Abin ban dariya, yaro ya tsinci hakori

Da yake bayani a garin Fatakwal, jihar Ribas, Mujaheed Dokubo-Asari ya ce abin ban dariya ne a ga Wike ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a Najeriya.

Kamar yadda mu ka ji a bidiyon, ‘dan jarida ya nunawa Asari cewa kowane ‘dan Najeriya yana da damar da zai fito takara ko kuma ya kada kuri’arsa a zabe.

Dokubo Asari
Mujahid Asari-Dokubo Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A nan ne sai aka ji ya ce al’umma za su yi amfani da PVC dinsu, domin zaben wanda suke so. An rahoto cewa Asari bai kyale har tsohon gwamna Peter Obi ba.

Leadership ba ta kawo wata hujja da Mujaheed Dokubo-Asari ya bada ba, sai dai kurum a ra’ayinsa bai ganin Gwamnan ya dace ya mulki ‘Yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

“Abin dariya ne a ce Wike ya na so ya zama shugaban kasa. Dube shi, shin yana kama da shugaban kasa?
“’Yan Najeriya za su yi sha’awar shugaban kasa irin haka?”
“Shi ma kan shi ya san ba zai yiwu ba. Eh, kowa yana da damar yin takara. Mu ke da katin zabenmu, za mu tantance mutumin da za mu zaba.”

- Mujaheed Dokubo-Asari

Jonathan ya yi hadari

A jiya ne aka ji tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan yi fitar da jawabi na musamman bayan tsira da ransa a hadarin da ya rutsa da shi.

Ibrahim Abazi da Yakubu Toma suka rasu a cikin tawagar tsohon shugaban, sannan ‘yan sanda biyu da suka samu rauni, su na jinya a wani asibiti a garin Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel