‘Yan siyasa 9 da suka dade su na takarar shugaban kasa, har yau ba a san da zamansu ba

‘Yan siyasa 9 da suka dade su na takarar shugaban kasa, har yau ba a san da zamansu ba

  • Irinsu Alhaji Atiku Abubakar sun fito takara ba sau daya ba, ba sau biyu ba a tarihin siyasar Najeriya
  • Baya ga Atiku akwai ‘yan siyasan da sun yi ta neman kujerar shugaban kasa, amma dai ba su dace ba
  • Wadannan mutane ba su shahara ba kamar tsohuwar matar Obasanjo, Mojisola Adekunle Obasanjo

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu ‘yan siyasan da sunansu bai ratsa gari ba, da sun taba fitowa takarar shugaban kasa akalla sau biyu ba tare da yin nasara.

1. Pat Utomi

Farfesa Pat Utomi ya nemi kujerar shugaban kasa a zaben 2007 da 2011 a karkashin jam’iyyun ADC da SDMP. Duk kuri’ansa ba su taba wuce 50, 00 a zaben ba.

2. Arthur Nwankwo

Arthur Nwankwo ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar PMP a zaben 2003 inda ya samu kuri’u 57, 000. A 2007 da ya sake jarraba sa’arsa ya samu kuri’a 24, 164.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

3. Emmanuel Okereke

A 2023, Emmanuel Okereke yana cikin wanda suka nemi takara, amma 0.07% na kuri’u kawai ya iya samu. A zaben 2007, ‘dan siyasar ya samu kuri’u kusan 27, 000.

4. Habu Fari

Habu Fari ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 1978, bai kai ko ina ba. Bayan nan Marigayin ya nemi takara a NRC a 1992, ya kuma sha kasa a NDP a zaben 2007.

5. John Dara

John Dara ya nemi takarar shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar National Transformation Party (NTP) a 2011. Ana tunanin ya na shirin sake takara a SDP a 2023.

Ana yin zabe
Masu zabe a Najeriya Hoto: www.vox.com
Asali: UGC

6. Dele Momodu

A zaben 2011, Dele Momodu ya na cikin wadanda suka yi takara da Goodluck Jonathan, amma kuri’a 26, 376 ya iya samu a NCP, yanzu ya na neman tikiti a PDP.

Kara karanta wannan

Rigingimu na neman ratsa PDP, ‘Ya ‘yan Jam’iyya su na zargin shugabanninsu da zagon-kasa

7. Mojisola Adekunle Obasanjo

Manjo Mojisola Adekunle-Obasanjo ta yi ta neman shugabanci a Najeriya. Marigayiyar ta yi takara a zaben 2003 da 2007, a gaba daya zaben da kuri’u 8, 000 ta tashi.

8. Chris Okotie

A zaben 2003 ne Chris Okotie ya fara harin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar JP. Daga baya ya yi takara a 2007 da 2011 a karkashin jam’iyyar hamayya ta Fresh Party.

9. Rochas Okorocha

Na karshe a rukunin shi ne Sanata Rochas Okrocha wanda tun 2003 yake neman zama shugaban kasa. A 2014 ya nemi tikitin APC, kamar yadda yake nema a 2023.

Takarar Tinubu a APC

A jiya aka ji labari cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya ki yi wa Bola Tinubu mubaya’a karara a kan maganar neman kujerar shugaban kasa da zai yi a jam’iyyar APC.

Malam Nasir El-Rufai ya fadawa Tinubu cewa sun san da burin shi na son zama shugaban kasar nan, don haka su na addu’ar Allah ya yi wa Najeriya zabi na kwarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel