Saraki, Tambuwal, Mohammed sun kulla yarjejeniya kan wanda zai zama mataimakin shugaban kasa a 2023
- Jiga-jigan PDP daga arewa na zawarcin Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta domin ya zama mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023
- Manyan masu fada a ji na PDP kamar Bukola Saraki, Gwamna Aminu Tambuwal da Gwamna Bala Mohammed sun tuntubi Okowa domin ya nemi wannan kujera
- Saraki ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugaba irin Okowa domin ceto ta daga wannan hali da ta shiga a karkashin gwamnatin APC
Delta - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun yi wata ganawar sirri da Gwamna Ifeanyi Okowa.
Jiga-jigan kuma masu neman takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bukaci Okowa da ya nemi takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023.
2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau
Jaridar The Guardian ta rahoto daga wata majiya cewa a wajen taron wanda ya shafe tsawon sa'o'i, yan siyasar sun ce Okowa ya cancanci ayi aiki tare da shi saboda tarin kwarewarsa.
A wani jawabi da sakataren labaran Gwamna Okowa , Olise Ifejika, ya saki, ya nakalto Saraki wanda ya jagoranci gwamnonin da dan kasuwa, Alhaji Mohammad Hayatu-Deen, zuwa taron yana cewa Najeriya na matukar bukatar shugabanni da suka cancanta domin fitar da kasar daga kangin talauci, rashin tsaro da rikice-rikice.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa a karkashin PDP, Najeriya ce kasa mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afrika, amma abun bakin ciki a yanzu kasar ta zama kan gaba wajen talauci da garkuwa da mutane a karkashin gwamnatin APC.
Jawabin ya nakalto Saraki yana cewa:
“Mun yi tattaunawa mai amfani sosai tare da gwamnan; mun yanke shawarar zuwa a matsayin mu hudu, wadanda ke neman shugabancin kasar a karkashin inuwar PDP.”
Okowa, a nashi martanin, ya jaddada muhimmancin kulla yarjejeniyar fahimtar juna don magance kalubalen da ke damun kasar.
A halin da ake ciki, Okowa ya bayyana cewa PDP na aiki tukuru domin ceto kasar daga mawuyacin halin da gwamnatin APC ta jefa ta a ciki.
Ya ce:
“PDP za ta iya karbar shugabancin kasa, amma dole mu zamo masu karfin gwiwa. Yan Najeriya sun sha wahala sosai kuma sun gaji, don haka ya zama dole mu basu karfin gwiwar cewa za a samu haske a karshe.”
Ya kara da cewa:
“Yayin da yan Najeriya ke jiran ganin abun da PDP za ta yi gabannin babban zaben 2023, ina jinjinawa masu neman takarar shugaban kasa guda hudu, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki; Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Bala Mohammed; da Alhaji Mohammed Hayatuddeen kan hada kai da suka yi.
“Na yarda cewa matakin da suka dauka zai karfafa mu, kuma zai taimaka wajen hada kan jam’iyyarmu yayin da muke aiki domin ceto Najeriya.”
Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye
A wani labarin, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci yankin Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, ya ce Allah ya fada masa cewa Atiku Abubakar ne zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba.
A ranar 23 ga watan Maris ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya ayyana aniyarsa ta shiga tseren shugabancin 2023 a hukumance a karkashin inuwar PDP.
Yan kwanaki bayan sanar da aniyarsa ta neman shugabancin kasar, kungiyar kasuwanci ta arewa maso gabas ta siya masa fom din takara na naira miliyan 40.
Asali: Legit.ng