Allah ya faɗa mun nice zan zama shugaba bayan Buhari, Wata mace ta shiga takara a 2023

Allah ya faɗa mun nice zan zama shugaba bayan Buhari, Wata mace ta shiga takara a 2023

  • Wata sabuwar yar takarar kujerar shugaban ƙasa a Najeriya ta bayyana ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APGA
  • Angela Johnson, ya sanar da cewa Allah ne ya umarce ta da ta fito takara domin ita ce zata gaji shugaba Buhari a 2023
  • Tace lokaci ya yi da mace zata jagoranci kasar nan tun da mazan da mutane suka zaɓa sun gaza kataɓus

Abia - Yar takarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APGA, Angela Johnson, ta ce lokacin zaɓen 2023 ne ya dace Najeriya ta fara samun shugaban ƙasa mace.

Misis Johnson ta yi wannan furucin ne ranar Alhamis a Sakatariyar AFGA dake Umuahia, yayin da ta bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a hukumance, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Yan takaran shugaban kasa a APGA.
Allah ya faɗa mun nice zan zama shugaba bayan Buhari, Wata mace ta shiga takara a 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A jawabinta tace:

"Mazan mu da aka zaɓa a matsayin jagororin ƙasar nan sun gaza, duk da an zaɓe su domin su yi mana aiki amma sai abun ya juye, su da ake tsammanin su yi aiki, su ake wa aikin."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yar takaran ta kuma bayyana damuwarta cewa ba bu wani cigaba da Najeriya ta samu na azo a gani tun bayan dawowar mulkin demokaraɗiyya a 1999.

"Ina karkashin ikon Allah ne domin na dawo da kyakkyawan fatan miliyoyin yan Najeriya, waɗan da suka cire tsammani daga gyara ƙasar su."
"Allah ne ya kawo shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma ya bar shi a Ofis har sanda zan bayyana."

Ta tabbatar wa shugaban APGA cewa zai kafa tarihin zama mutum na farko da zai kawo shugabar ƙasa mace a Najeriya.

An mun tayin mataimakiyar shugaba

Johnson ta ce manyan yan siyasa daga manyan jam'iyyun ƙasar nan sun bukaci ta zama abokiyar takararsu a matsayin mataimakiya, amma ta yi watsi da tayin saboda Allah ne ya aiko ta.

"Allah ya mun magana, kuma naji yana cewa ya tura ni na zama shugabar ƙasa ba wai mataimakiya ba. Lokaci na ne, kuma lokacin matan Najeriya ne su samar da shugaba."

Kara karanta wannan

Yadda zan jagoranci jam'iyyar APC ta samu nasara a 2023. Sanata Adamu ya magantu

"Kishin ƙasa na cinye ni ta ciki, har zuwa san da martabar Najeriya za ta dawo, ba zan runtsa ba."

Yar takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya wacce ta fito daga jihar Abia, ta ce burinta shi ne ta taimaki al'umma kuma wannan ne abin da ta sa a gaba.

A wani labarin kuma Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar APC

Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Gombe, Abubakar Sadiq Ibrahim Kurba, ya yi murabus daga APC.

Ƙurba, wanda takwarorinsa mambobin majalisa suka tsige a 2020, ya ce ya ɗauki matakin ne bisa wasu dalilai na ƙashin kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262