2023: Atiku, Tambuwal da sauran jiga-jigan PDP sun gana don gina yarjejeniya kan dan takarar shugaban kasa
- Jiga-jigan yan PDP da ke neman kujerar shugaban kasa na ci gaba da fafatawa kan yankin da jam'iyyar za ta baiwa tikitinta
- Manyan masu neman kujerar a yankin arewacin kasar na zurfafa tattaunawa domin fitar da dan takarar yarjejeniya
- A yanzu haka an sa labule tsakanin Atiku Abubakar, Saraki, Tambuwa, Bala Mohammed da Hayatudeen don cimma matsaya guda
Abuja - Manyan yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun sake ganawa don tatauna ra’ayinsu yayin da ake ci gaba da muhawara kan yankin da jam’iyyar za ta baiwa tikiti gabannin babban zaben 2023.
Har yanzu dai babbar jam’iyyar adawar kasar bata bayyana yankin da za ta baiwa tikitinta na takarar kujerar ta daya ba, yayin da yan takara ke ci gaba da zawarcin kujerar.
Yayin da yan siyasar kudu ke kokarin ganin an mika tikitin zuwa yankinsu, takwarorinsu na arewa ma na so a mallakawa yankinsu tikitin, lamarin da ka iya kawo sauyi a al’adar jam’iyyar na yin karba-karba.
Tsawon shekaru da dama, jam’iyyar na bin tsarin shiyya-shiyya tsakanin yankunan biyu, matsayin da sabon shugabancin ya yi alkawarin ci gaba da shi yayin da zaben 2023 ke kara matsowa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A zaben karshe da aka yi, yankin arewa ta miukawa tikitin inda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya daga tutar jam’iyyar a zaben na 2019.
Sai dai kuma, Atiku ya sha kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke kan karagar mulki a lokacin.
Yayin da suka yi biris da wannan matsayi, manyan yan takara sun yi wata ganawar wacce ta samu halartan Atiku Abubakar, Bukola Saraki; Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da takwaransa na jihar Bauchi, Bala Muhammad.
Sun yi ganawar ne a ranar Litinin, 28 ga watan Maris inda suka tattauna batun hada karfi da karfe wajen fitar da dan takarar yarjejeniya.
An yi irin wannan ganawar kwanaki biyar da suka gabata inda dukkansu suka hallara sai dai Atiku da baya wajen.
Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
“Na yi wata ganawa da @bukolasaraki, Tambuwal, @SenBalaMohammed da Hayatudden a daren yau don tattauna makomar jam’iyyarmu da Najeriya. Ina duba zuwa ga ci gaba da tattaunawarmu da ginda #Najeriyadaya."
Saraki da Mohammed sun yi Karin bayani a kan ganawar sa’a daya bayan Atiku ya yi.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya wallafa a shafinsa cewa:
“A daren yau, tare da Gwamna @AWTambuwal, Gwamna @SenBalaMohammed, da Alhaji Mohammed Hayatuddeen, mun ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji @Atiku Abubakar don tuntubar shi game da tattaunawar da muke yi kan tsayar da dan takarar yarjejeniya a jam’iyyarmu ta @OfficialPDPNig mai albarka.”
Tun kafin a je ko ina, PDP ta samu kusan Naira miliyan 300 daga saida fam din takara
Agefe guda, mun ji cewa akalla Naira miliyan 285 su ka shigo hannun jam’iyyar hamayya ta PDP daga wajen ‘yan takara takwas da su ke sha’awar takarar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta ce daga lokacin da majalisar NEC ta PDP ta amince a soma saida fam zuwa yanzu, har an samu kudin da ya haura Naira miliyan 200.
Zuwa ranar Talatar nan (29 ga watan Maris 2022), abin da aka tara daga mutanen da suke neman a ba su tutan jam’iyyar hamayyar shi ne Naira miliyan 280.
Asali: Legit.ng