Zan janye daga takarar shugaban ƙasa bisa sharaɗi ɗaya, Gwamnan dake mafarkin gaje Buhari a 2023

Zan janye daga takarar shugaban ƙasa bisa sharaɗi ɗaya, Gwamnan dake mafarkin gaje Buhari a 2023

  • Gwamnan jihar Ribas kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce zai iya janye kudirinsa matukar PDP ta nemi hakan
  • Nyesom Wike, wanda ya bayyana shirinsa na neman kujera lamba ɗaya ranar Lahadi, ya ce zai yi wa jam'iyya biyayya
  • A cewarsa, matukar PDP ta yanke ba ɗan arewa tutar takara, ba zai ja da jam'iyya ba saboda ta masa komai

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace zai janye daga takarar shugaban ƙasa matukar PDP ta yanke kai tikiti yankin arewa.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata fira da kafar watsa labarai ta Channels Tv, ranar Litinin.

Domin shawo kan lamarin tsarin karba-karba, jam'iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin mutum 37 wanda zai duba yankin da ya dace ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mun dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna har ila ma sha'a Allahu, NRC

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Zan janye daga takarar shugaban ƙasa bisa sharaɗi ɗaya, Gwamnan dake mafarkin gaje Buhari a 2023 Hoto: Adeyanju Deji/facebook
Asali: Facebook

A ranar Lahadi, Gwamna Wike ya bayyana shirinsa na neman kujerar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Da yake jawabi kan cigaban, Wike ya ce ya yi amanna da PDP kuma a shirye yake ya bi duk hukuncin da ta yanke game da wanda zata ba tuta a 2023.

The Cable ta rahoto gwamnan na cewa:

"Ni mutum ne mai saukin kai, ba abun da zai sa na saɓa yarjejeniya saboda mulki, ko an rubuta ko ba'a rubuta ba, domin haka ne halin cikakken mutum."
"Kamar a ce a yanzu, jam'iyyar PDP ta fito tace ta yanke baiwa ɗan arewa tikitin takara, bani da matsala da haka."

Idan PDP ta kai takara Arewa wane mataki Wike zai ɗauka?

Da aka tambaye shi, ko zai cigaba da neman cika mafarkinsa idan PDP ta yanke kai takara Arewa, Gwamna Wike ya ce:

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun tada Bam kan jirgin kasa Abuja-Kaduna mai dauke da fasinjoji 900

"Ba zan nema ba, zan yi wa jam'iyya biyayya, amma abun da ba zan yarda ba shi ne mutane su ce ba zancen tsarin karɓa-karba. Wannan dalilin ne ya sa ban taɓa barin PDP ba tun 1998."
"PDP ta bani komai, saboda haka kan wani abu ba zan taɓa barinta ba, bani da wurin zuwa, ba wata jam'iyya da zan koma, ba zan iya barin PDP ba."

A wani labarin kuma Yan takarar shugaban ƙasa uku a PDP sun haɗa sabuwar tafiya, sun shirya kwace mulki a 2023

Yan takarar kujerar shugaban ƙasa uku karkashin inuwar PDP sun haɗa kan su, sun shirya yin sulhu domin kwace mulki a 2023.

Jiga-Jigan siyasar uku sun ziyarci gwamna Ortom na jihar Benuwai domin neman goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262