Duk da ‘Dan takararsa bai yi nasara ba, Tinubu ya taya Adamu murnar zama Shugaban APC

Duk da ‘Dan takararsa bai yi nasara ba, Tinubu ya taya Adamu murnar zama Shugaban APC

  • Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da jawabi na musamman bayan an yi zaben shugabannin APC na kasa
  • Jigon jam’iyyar mai mulki ya yabi sabon shugabansa Abdullahi Adamu, ya ce ‘dan siyasa ne irinsa
  • Bola Tinubu ya yi kira ga Adamu da sauran wadanda aka zaba su dage wajen kai APC ga nasara

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu ya taya Abdullahi Adamu murnar zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa a Najeriya.

The Cable ta ce Bola Tinubu ya fitar da jawabi na musamman, yana taya Adamu murnar cin zabe.

Hakan na zuwa ne bayan Sanatan na kudancin jihar Nasarawa ya yi nasarar zama shugaban APC na farko bayan kusan shekaru biyu babu tsayayyen shugaba.

Kara karanta wannan

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

Da yake magana a jawabin na sa, Tinubu ya ce hikimar Sanata Abdullahi Adamu za ta zama babbar kadarar APC yayin da za a shiga lokacin babban zabe.

Bola Tinubu wanda yana cikin jiga-jigan APC a Najeriya, ya yi kira ga sababbin ‘yan majalisar NWC su yi aiki domin tafiyar da jam’iyyarsu zuwa ga ci.

Dole a yabawa Buhari da CECPC

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci yabo na jagorancinsa. Sauran wadanda suka dace da jinjina su ne kwamitin CECPC na rikon kwarya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban APC
Bola Ahmed Tinubu da Sanata Abdullahi Adamu Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

“Mun yaba da irin mutanen da aka zaba domin su rike mukamai a jam’iyyar nan kamar yadda suka yi rantsuwa. Mu na kira da su yi aiki domin hada-kan jam’iyya.”
“Idan aka yi haka, jam’iyyar APC za ta kai ga nasara, za a samu shugabanci mai kyau a kasa.”

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Adamu 'dan siyasa ne iri na - Tinubu

“Ina taya sabon shugaban jam’iyya, Alhaji Abdullahi Adamu wanda mutum ne iri na; mai kafa tawaga kuma tsohon gwamna, tsohon shugaba, kwararren dattijo.”
“Ina taya duk wani ‘dan jam’iyya da aka ba sabon mukami, ina yi masu fatan alheri a aikinsu.”
“Dole sababbin shugabanni da ‘ya ‘yan jam’iyya su hada-kai domin ganin jam’iyyar APC ta sake samun gagarumar nasara a kowane mataki a zaben 2023.” - Tinubu

A karshen jawabin Tinubu, an rahoto yana cewa cigaban kasar nan ya dogara ne da nasarar APC.

Tinubu a zaben APC

Ku na da labari cewa Bola Ahmed Tinubu ya rasa kujeru biyu daga cikin wadanda aka warewa yankinsa a NWC. Amma ya tashi da kujerar shugaban matasan APC.

Sannan kuma ana tunanin Bola Tinubu ya so a ce Tanko Al-Makura ne ya lashe wannan zaben. A wani kaulin kuma ana zargin yana tare ne da Sanata George Akume.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel